Jan hankali ga kungiyoyin Izala da Shi’a (2)

Wannan tsokaci mai take na sama, an gabatar da shi a  shekarar 2014, shekara biyar ke nan da ta gabata. GIZAGO ya samo shi ne daga turakar hazikin marubuci, MALAM AUWAL KANO (08064595353). Muhimmancin abubuwan da aka tattauna ya sa aka bijiro da shi, inda a makon jiya muka wallafa kashi na farko na tsokacin, […]

Jan hankali ga kungiyoyin Izala da Shi’a (2)

Wannan tsokaci mai take na sama, an gabatar da shi a  shekarar 2014, shekara biyar ke nan da ta gabata. GIZAGO ya samo shi ne daga turakar hazikin marubuci, MALAM AUWAL KANO (08064595353). Muhimmancin abubuwan da aka tattauna ya sa aka bijiro da shi, inda a makon jiya muka wallafa kashi na farko na tsokacin, sannan muka tsakuro martanonin wadansu daga cikin al’umma. A wannan karo za mu ci gaba da kashi na biyu, kamar haka:

 

Bari mu bude da ta’alikin Lawan Muhammad PRP: “Kowace daga cikinsu tana bukatar Auwal ya bincika asasin da ya kafa ta kafin ya yi sharhi. Sai na ga kamar malamin ya yi gaggawar fitar da rubutun. Waccan fa sunanta kungiyar kawar da bidi’a da tsaida Sunnah. Ka ga ke nan yakinsu a nan ya tsaya. Ban san ko za a kira Shi’a kungiya ba amma mafi yawan manufofinsu jihadi ne, babu ruwansu da wata bidi’a ko tsaida Sunnah. To sai dai in mutum yana son samun saukin fadarsu sai ya ce kungiyoyi. Da fatar Malam Auwal zai bincika.”

Ita kuwa Ummi Usman, ba dogon sharhi ta yi ba, ga abin da take cewa: “Hmm, Auwal ke nan! Har kiran ’yan Shi’a kake yi su musuluntar da mutane? Allah Ya kyauta!”

Ga alama dai tsokacin Auwal bai yi wa Saleh Aliyu dadi ba, domin kuwa shi dogon ta’aliki ya yi masa, yana cewa: “Yanzu kam Malam Auwal, kibiyarka ta nuna inda ta dosa sosai. Na jima ina bin sawun duk rubuce-rubucen da kake ta yi, musamman wadanda suka shafe mu. Na ga kamar ba bukatar in mayar maka da martani ne saboda ina ba ka uzuri; kamar da nufin maslaha da neman gyara kake yi. Amma lallai ina da mulahazozi da yawan gasken-gaske a rubuce-rubucenka irin su ‘Zuwa ga Almajiran Malam Zakzaky’ na 1 da na 2 da ka yi tsokaci kan abubuwan da ka yi tsokaci a kai; duk da yake kai dalibin aikin jarida ne kuma a rubuce-rubucen kana so ka nuna kamar ba ka da bangare ne, kamar kai dan-ba-ruwanmu ne, amma ga wanda ya san abin da yake yi, ya kuma nazarci inda bakinka ya karkata, yake kuma da masaniya a aikin jarida, lallai zai fahimci inda kibiyar rubutun naka ta fuskanta.

“Abin takaici, a duk rubuce-rubucen nan naka ka takaita kanka matuka wajen bincike da bin diddigi, kamar yadda kuma ka nisanta kanka ga su ’yan uwa almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) din, balle ka ji ta bakinsu kafin ka yi duk wani rubutu a kansu. Hausawa dai suna cewa karamin sani kukumi ne. Kawai ka dogara ne da ’yar kuntatacciyar fahimtarka a kansu. Amma a wannan karon sai maitarka ta sake fitowa fili, hatta wadanda suke ba ka uzuri irina, sai muka fahimci irin yadda rashin adalcinka ga ’yan Shi’a ya bayyana tamkar hasken rana.

“Da yake ’yan Shi’ar nan ba a duniyar wata suke ba, su kuma almajiran Sheikh Zakzaky (H) ba a wata kasa suke ba, zai yi kyau duk wani abu da ba ka da masaniya game da su, ko kuma ka ga suna aikatawa, kuma kana so ka yi rubutu, maimakon ka zo kana hukunta su bisa jahilci, ko kuma bisa abin da wadansu tsiraru, wadanda kai da kanka ka kira su ’yan caji-caji da suka rubuta a Facebook suka rubuta, ya kamata ka binciki masu sassaucin ra’ayinsu, masana daga cikinsu, wadanda aka yarda za su iya yin magana da yawunsu, ka kusance su; su za su warware maka zare da abawa a kan duk wata kadiyya da kake son yin tsokaci a kanta. Amma ka zo kana cewa: “Ya kamata almajiran Zakzaky su sani bukukuwan da suke yi ba su ne Musulunci ba.” Ko kuma ka zo kana cewa: “Yan Shi’a har zuwa yanzu ba ni da masaniya ko suna da makamancin irin kwamitocin da ’yan Izala suke da su na musuluntar da Maguzawa da yada ilimin addinin Musulunci.” Wannan babbar kasawa ce a farfajiyar aikin jarida, kuma kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba.

Ban san ko don a Darus Salafiyya ka yi karatu ba, kuma ’yan Izalar su ne mafiya yawan abokanka, kuma har sukan yi maka takakkiya su karanta maka doguwar wasika a duk lokacin da suka lura kamar kana neman ka karkata zuwa bangaren darika, ko kuma ka zama dan-ba-ruwanmu, shi ya sa ka fahimci cewa: “Kungiyar Izala gaskiya suna kokari wajen aikin musuluntar da Maguzawa, suna matukar kokari wajen shiga kauyuka da yada ilimin addinin Musulunci.” Amma su kuma ’yan Shi’a ba ka san abin da suke yi ba, ban da bukukuwa, wanda su kuma ka ce ba Musulunci ba ne?

“Na yi tsammanin kasancewarka da mutane irin su Malam Muhammad Ibrahim Kaduna zai taimaka maka wajen daidaita fahimtarka, har ka fahimci inda duniyar Shi’a ta fuskanta da kuma irin aikace-aikacen da suke yi, wadanda suka yi hannun riga da irin tunaninka. Don haka ‘Gaskiya akwai bukatar ka sake lale’ abokina.

“Amma lallai yanzu mun fahimci “ka fake ne da guzuma ka kashe karsana…” kamar yadda Kabiru Usman Hussaini ya fada. Wannan kuwa “ya gwada kana da gefe, abin da kuma ya saba ka’idar dan jarida ko marubuci,” kamar yadda Abdulhamid Muhammad Sani ya fada.”

Ita kuwa Ummu Husna MB, fyadar ’ya’yan kadanya ta yi wa kowa, inda ta yi nasiha da cewa: “Jama’a a cire son rai, kowa ya bi Alkur’ani da Sunnah, a karantar da mutane gaskiya kuma a yi aiki da ita bisa koyarwar Manzon Allah (SAW). Duk abin da aka ce kungiya ce, to wallahil azimu sai an samu son rai ko da kadan ne. Ya Allah! Ka ganar da mu gaskiya, Ka ba mu ikon aiki da ita bisa koyarwar Annabi Muhammad (SAW).”

Ibrahim Garba Nayaya kuwa beken Auwal ya gani, inda ya yi masa raddi da cewa: “In mafadin magana wawa ne… Cikin wannan sharhi ba abin da zan ce face bayyana wa Malam Auwal kura-kuran da yake tafkawa a rubuce-rubucensa, musamman a kan abin da ya shafi akida. Shin kana tsammanin za a gauraya tsakuwa da shinkafa a wuri guda, sannan a ce su ciwu? A matsayinka na wanda kake da’awar kana zantawa da Dokta Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, bai kamata kana irin wannan kwamacalar ba. Duk mutumin da ya yi karatu ko yake karatu kuma karatun da natsuwa da hankali, yake karanta tarihi; ya san tushe na wadannan kungiyoyi. Kowa ya san wanda ya assasa Shi’a kuma kowa ya san inda akidunsu suka dosa. Da wannan ne mafi yawan malamai suke kore danganta ta da Musulunci. Kai da kanka ka sha yin rubutu a kan munanan akidunsu Shi’a da kuma yadda suke kafirtar da duk wanda ba dan Shi’a ba ne da kokarin kashe su da kafirta sahabbai. Shin Izala tana haka? Ka ji tsoron Allah ka daina yada irin wadannan gurbatattun tunani a tsakanin al’umma.”

Daga nan kuma sai Sani Mutum ya biyo baya da nasa ta’alikin da yake cewa: “Ba ka taba tafka babban kuskure a rubutunka da take gaskiya ba kamar yau. Gaskiya Auwal ka ban mamaki har da kake tunanin hadin kai zai samu tsakanin masu kafirta matan Annabi da sahabbansa. Wanda yadda kafiri zai yi kalmar shahada yayin shiga Musulunci, haka wanda zai shiga Shi’a zai la’anci Abubakar da Umar da Usman da A’isha da Hafsa, ya kuma tabbatar da kasantuwarsu a wuta. Ina da faifan bidiyo na gani a wajena. To ta yaya mutum zai hada kai da wadannan batattu. Annabi (SAW) ya tabbatar da cewa wadannan bayinSa ’yan Aljanna ne, wani katon banza ya ce ’yan wuta ne, ya karyata Manzon Allah (SAW); yaya za a yi ka hada kai da shi? Kuma duk ka san wadannan akidu nasu munana da wadanda ban kawo ba amma don son zuciya ka ce wai a hada kai da su. Ai ba ’yan Izala ba, hatta ’yan darika na gaske ba za su hada kai da Shi’a ba.”

Za mu ci gaba