Jan hankali game da ‘Kifayen Annabi Ibrahim’

Daga Uba Ahmad Ibrahim Jos (07061587787) muka samu wannan tsokaci mai jirwaye da ruwan tarihi da jan hankali, wanda ke cewa: kasar Turkiya na daga cikin kasashen yankin Gabas Ta Tsakiya da suka shahara wajen tarihi da kissoshi masu daukar hankali matuka gaya. Daga cikin muhimman kissoshin da ba za a manta da su ba, […]

Jan hankali game da ‘Kifayen Annabi Ibrahim’
Jan hankali game da ‘Kifayen Annabi Ibrahim’

Daga Uba Ahmad Ibrahim Jos (07061587787) muka samu wannan tsokaci mai jirwaye da ruwan tarihi da jan hankali, wanda ke cewa:

kasar Turkiya na daga cikin kasashen yankin Gabas Ta Tsakiya da suka shahara wajen tarihi da kissoshi masu daukar hankali matuka gaya. Daga cikin muhimman kissoshin da ba za a manta da su ba, akwai kissar haihuwa tare da rayuwar Annabi Ibrahim [AS].
A wani gari mai suna Urfah da ke cikin kasar ta Turkiyan aka haifi Annabi Ibrahim [AS], a nan kuma ya taso har ya kai ga samun annabta. A cikin garin ya dinga kiran babansa da sauran mutane su bar bautar gumaka da ba sa ji ba sa gani ba kuma za su iya amfanar da kansu ko cutar da kowa ba. A nan ne kuma daga baya da ya tabbatar da cewar ba za su yi imani ba, ya farfasa gumakan nasu, kamar dai yadda ayoyin Alkur’ani Mai girma suka bayyana mana, har aka kai lokacin da sarkin garin, Namarud
ya shirya hallaka Annabin namu, ta hanyar haka rami da hura wuta da kuma jefa shi a ciki da nufin ya mutu su huta.
Allah Ta’ala kuma Ya tserar da shi, Ya sa wutar ta zamo mai sanyi da aminci gare shi. Wannan abu ya faru ba kokwanto ko miskala zarratin a zukatan Musulmi game da shi. Amma abin da ke faruwa yanzu a wancan gari na Urfah shi ne, inda ake ci gaba da yayata abin tare da kawo kissoshi na ban al’ajabi game da wani dan karamin rafi a cikin garin mai cike da kifaye, inda kissoshin ke cewa ramin da aka haka ke nan tun wancan lokacin da nufin hallaka Annabi Ibrahim [AS], wutar da aka hura a lokacin ce ta zamo ruwan, yayin da itatuwan kuma suka zamo kifayen.
Masu yawon bude idanu kuwa kullum sai kara kwarara zuwa garin suke yi, domin ganin rafin da kuma sauran wuraren da Annabi Ibrahim [SA] ya rayu a farkon rayuwarsa.
Batun a ce kakar kifayen da ke rayuwa cikin wannan rafi ta yanke saka bai taso ba, domin kuwa duk wanda ya je wajen sai ya zuba musu abinci, farautarsu kuma haramun ne, domin a cewar masu shararata; duk wanda ya ci namansu to wutar ce za ta kona masa cikinsa; nan take ya fadi ya mutu. Har yanzu kuma ba a sami wanda ya ce bari ya yi ta maza ya gwada cinsu ba.
Ba kifayen kadai ba, su kansu masu harka a wajen, kakarsu yanke sakar ta yi; domin kuwa a kullum ba su da aiki in ba kirkiro sabbin kissoshi na ban al’ajabi game da wurin da nufin samun karin maziyarta da samun kudaden shiga ba.
Kogon da aka tabbatar da cewa a cikinsa ne aka haifi Annabi Ibrahim [AS] kuwa, a kullun cike yake da masu ziyara har ma kuma an gina dan karamin masallaci a wajen da mutane za su iya alwala su yi Sallah. Duk da cewa hukumar Turkiya ta gargadi Musulmin da ke zuwa wajen game da fadawa cikin bidi’a da sabon Allah da sunan neman tabarruki da wajen, to amma da alama ihunka-banza take yi, domin kuwa masu tabarruki da wani idon ruwa da ke fitowa daga cikin kogon suna nan bila adadin; har ta kai ga duk wanda ya samu kai wa gare shi ya yi alwala ko ya sha, to in ya tashi fitowa sai dai ya fito da baya amma ba dai ya juyo ya daina fuskantarsa ba, duka wai domin kara samun albarka da makamantan hakan.
Ziyartar wuraren da aka haifi Annabawan Allah kamata ya yi ta zamo domin kara daukar darasi da karin imani, amma bisa ga dukkan alamu irin yadda lamarin ke gudana a wasu daga cikinsu, ya zamo wata dama ce ga wasu su dinga shararata domin su dinga samun damar cika aljihunsu a kowacce rana, ba tare da la’akari da hakikanin gaskiya ko kuma me zai biyo baya nan gaba ba.
***
Kafin a kama Janar Buhari
Shi kuwa Aminu dankaduna Amanawa Sakkwato (07065654787), tsokaci ya yi game da kitimirmirar da ake kitasawa ga Janar Buhari. Ga abin da yake cewa:  
A kwanan baya ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya bukaci da a soke wadansu kungiyoyi, cikinsu kuwa har da CAN, wadda ya bayyana ta a matsayin kungiyoyin da kan iya haddasa fitina a kasa! To yanzu ta dai ta fito fili, kungiyar barazana ce ga zaman lafiya a Najeriya.
Na bayyana haka ne sakamakon yadda sakataren kungiyar na kasa ya fito kafafen watsa labarai ba kunya ba tsoron ido, yana kira da a kame tauraron talakawan Najeriya Janar Buhari, a kan wata hira da aka yi da shi a daidai lokacin da shugaban kungiyar Tsirarun Neja-Delta ke ci gaba da fadin abubuwan da ya kamata a ce tuni yana gidan kaso, amma kuka yi shiru ba ku ce kanzil ba. To ku sani, Janar Buhari ba ya neman tashin hankali kuma ba ya umarni a tada hankali, amma kama shi ba za ta haifar wa kasarmu da mai ido ba.
***
Sanarwa: Gizagawan Jihar Filato za su gudanar da taronsu a jibi Lahadi, a Habib Restaurant da ke titin zuwa Bauchi, da misalin karfe 3:00 na rana. Domin karin bayani, a tuntubi PRO, Rabi’u Baban Amira 08033512622.
A labarin jajantawa kuwa, mun samu labarin cewa Allah Ya yi wa Malam Auwalu Yellow, mai sayar da jarida a Babban Masallacin Juma’a Abuja rasuwa. Ya rasu ne bayan doguwar jinya da ya sha. Ya rasu ya bar matar aure daya da ’ya’ya. Allah Ya jikansa da rahama, Ya dayyaba zuri’ar da ya bari a baya. Mu kuma da muka rage, muna rokon Allah Ya ba mu ikon cikawa da ingantaccen imani, idan namu lokacin ya zo. Amin, amin!