Ishola Williams: Janar ɗin da ya yi ritaya ba shi da ko sisi
Janar Ishola Williams, ya ce zai fi so ya kasance ɗan wata kasa daban ba Najeriya ba
Tsohon Janar din sojan Najeriya, Ishola Williams mai ritaya ya ce a lokacin da ya yi ritaya daga aikin soja bai mallaki ko sisin kwabo a asusnun ajiyarsa na banki ba.
Janar Ishola Williams, ya ce zai fi so ya kasance ɗan wata kasa daban ba Najeriya ba.
Janar Williams wanda ya shiga aikin soji a shekarar 1964, har ya kai matsakin Kwamandan Rundunar Horarwa da Dokoki Aikin Soja (TRADOC), Rundunar Sadarwa da kuma Babban Jami’in Horarwa da Tsare-Tsare na Tsaro, ya bar aiki ne a a shekarar 1993.
A wata hira da Trust TV, tsohon kwamandan sojin ya ce zai fi so a ce shi ɗan asalin a kasar Namibiya ne ba Najeriya ba, saboda Namibiya kasa ce karama amma tana da tsari.
- Ya ƙone budurwa saboda ta ƙi auren shi
- DAGA LARABA: Abin Da Gwamnati Za Ta Yi Idan Tana Son Hana Zanga-Zanga
Yayin da yake bayar da labarin rayuwarsa ta baya, Janar Ishola Williams ya ce ya bar aikin soji ba tare da wani tsari ba kuma ba tare da ya tara kudi a asusunsa na banki ba, duk da cewa yana bukatar kudi don kafa wata kungiyar jinƙai.
“Na bar soji a ranar 20 ga Nuwamba ko wani lokaci a shekarar 1993, kuma sai na yanke shawarar abin da zan yi da kaina.
“Na bar soji ba tare da wani tsari ko shiri ba, ga shi kuma ba ni da kudi a bankina” in ji shi.
Ya ci gaba da cewar “Wasu mutane sun yi kokarin taimaka min.
“Akwai wanda ya ba ni mota, sai dai kuma tana da matsala, don haka sai na watsar da ita na koma shiga jirgin ƙasa.
“Wasu mutane sun ba ni ofis da zan iya zama a ciki don aiki na wani lokaci, yayin da wasu ke ƙoƙarin ƙarfafa min gwiwa don fara kasuwanci.
“Daga cikinsu akwai wani wanda ya ƙarfafa min gwiwa don zama bmai rarraba siminti, amma kuma sai na ajiye kudade masu yawa.
“To sai dai kuma asusun bankina babu ko Naira guda a ciki, don haka ta ina zan iya ajiyar kudade masu yawa?
“Akwai wasu abubuwa da yawa makamantan haka da suka faru.
“Abin mamaki, wasu mutane a Arewa ne suka yi ta kokari da shirye-shiryen ƙarfafa min gwiwa don in fara harkar kwangila.
“Amma abinci, mutanena na Kudu tambaya ta suke yi, cewa ina nake lokacin da abokaina suke samun kudi?
“Ai na san cewa zan gudanar da wata kungiyar agaji, kuma ina bukatar kudi don yin hakan.
“Don haka na ce wa kaina, idan zan samu kwangila zan iya amfani da abin da na samu don gudanar da kungiyar. Ba na sha’awar kasuwanci don samun riba.
“Haka na fara gudanar da wannan kungiya; muna gudanar da ayyuka.
“To amma samun mutane su bayar da bayani da lissafin kudaden da aka kashe da kuma tabbatar da cewa an yi komai yadda ya dace, ko da kuwa malamai ne, yana da wahala.
“Sai ’yan kaɗan ne suke bin ka’ida. Wasu sun mutu ba tare da bayar da lissafi ba, wasu har zuwa kotu muka yi.”
Ya tuna yadda membobin NGO ɗin da ya yi aiki da su suka tilasta masa cewa “Gaba ɗaya zan dawo a matsayin dan kasar Namibia, ba a matsayin dan Najeriya ba.”