Janar Alkali: ’Yan sanda na neman Dagacin Du da wasu mutum 7 ruwa-a-jallo
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta bayyana cewa tana neman Dagacin Dura a lardin Du da wadansu mutum bakwai ruwa-a-jallo sakamakon ganowa da ta yi cewa suna da hannun wajen bacewar Manjo-Janar Mohammed Idris Alkali (mai ritaya). Rundunar ’Yan sandan ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa wadanda take nema ruwa a […]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta bayyana cewa tana neman Dagacin Dura a lardin Du da wadansu mutum bakwai ruwa-a-jallo sakamakon ganowa da ta yi cewa suna da hannun wajen bacewar Manjo-Janar Mohammed Idris Alkali (mai ritaya).
Rundunar ’Yan sandan ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa wadanda take nema ruwa a jallon suna da hannu wajen kitsawa da garkuwa da kuma bacewar Janar Alkali da aka daina jin duriyarsa tun a ranar 3 ga Satumba, 2018.
A cikin wadanda ake nema akwai Yakubu Rap, baki, mai kimanin shekara 52, wanda shi ne Dagacin Dura Du, gundumar da ake zargin a nan Janar Alkali ya bace.
Rundunar ta annaya sunayen mutanen da ake zargin ne a cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta, DSP Tyopev Terna da ta fitar a jiya Laraba.