Janar Bamaiyi ya koka kan yadda gwamnati ta kasa kawo karshen kashe-kashe a Arewa

Tsohon Babban Hafsan Sojojin Najeriya a lokacin mulkin Janar Sani Abacha, Janar Ishaya Bamaiyi ya koka kan yadda Gwamnatin Tarayya ta kasa kawo karshen kashe-kashen al’umma da ake yi a Arewancin kasar nan.  Janar Ishaya Bamaiyi ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen bikin bude wata sakatariyar […]

Janar Bamaiyi ya koka kan yadda gwamnati ta kasa kawo karshen kashe-kashe a Arewa
Janar Bamaiyi ya koka kan yadda gwamnati ta kasa kawo karshen kashe-kashe a Arewa

Tsohon Babban Hafsan Sojojin Najeriya a lokacin mulkin Janar Sani Abacha, Janar Ishaya Bamaiyi ya koka kan yadda Gwamnatin Tarayya ta kasa kawo karshen kashe-kashen al’umma da ake yi a Arewancin kasar nan.  
Janar Ishaya Bamaiyi ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen bikin bude wata sakatariyar cocin UMCA Church da ke garin Zuru a Jihar Kebbi, inda ya ce dole ne Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin kawo karshen kashe-kashen al’ummar kasar nan da ake yi kullum ba kakkautawa, ganin yadda mahara ke zuwa su kai hari su kashe mutane su tafi ba tare da an kama kowa ba, duk da dokar ta-baci da aka sa a jihohin Borno da Adamawa da Yobe.   
Janar Ishaya ya ce Najeriya ta sha tura dakarunta zuwa kasashen duniya don kwantar da rikice-rikice kuma sun samu nasarori masu yawan gaske, amma abin ya gagara a cikin kasar nan. “Wannan abin dubawa ne kuma abin tunani ne, kuma akwai alamar tambaya ga jami’an tsaro da kuma gwamnati. Abin da mamaki a ce muna da jami’an tsaro na farin kaya (SSS), wadanda za su iya bincike kan lamarin domin gano wadanda suke taimaka wa maharan da wuraren da suke samo makaman da suke amfani da su,” inji shi.
Ya ce idan gwamnati ba ta dakatar da rikicin ba, to, lallai ba da gaske take yi ba, “Babu yadda za a ce wadansu mahara sun fi karfin gwamnati tunda ba yaki ba ne a tsakanin wata kasa da wata kasa. Ya kamata gwamnati ta dauki matakin da ya dace kada a durkusar da kasar nan, muna ji muna gani,” inji shi.
Janar Bamaiyi ya ce shugabannin da suke ganin kamar talakawa abin ya fi shafa, to su ma nasu na zuwa idan ba su dauki wani kwakkwaran mataki ba, domin Allah ba azzalumin kowa ba ne duk abin da mutum yake yi Yana kallonsa.