Janar Buhari a mahangar dimokuradiyya

Dubun dubatan jama’an da suka hallara a Abuja a ranar Laraba sun ji waka daga bakin mai ita, sun kuma fahimci inda aka dosa da jan aikin da ke gaban magoya bayan Janar Muhammadu Buhari, domin kuwa abin na yi don a tserar da kasar nan daga turbar halaka da gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ta […]

Janar Buhari a mahangar dimokuradiyya
Janar Buhari a mahangar dimokuradiyya

Dubun dubatan jama’an da suka hallara a Abuja a ranar Laraba sun ji waka daga bakin mai ita, sun kuma fahimci inda aka dosa da jan aikin da ke gaban magoya bayan Janar Muhammadu Buhari, domin kuwa abin na yi don a tserar da kasar nan daga turbar halaka da gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ta dora ta, hakan kuma ya jefa jama’an cikinta cikin bakar ukubar da ba su taba shiga ba. To yanzu dai an kashe bakin tsanya, masu cewa Janar Buhari bai kamata ya tsaya ba, saboda ya sha fafatawa, ana kayar da shi, da wadanda suke cewa kamata ya yi ya ja can gefe guda, ya daga hannun wani matashin da suke ganin shi ya fi cancanta, sai su sake dabara: Janar Buhari dai ya fito, kuma tamkar wata a daren farko na fitowarsa, jama’a sun taru don kallonsa, sun kuma amince su rufa masa baya a doguwar tafiyar da zai yi, kuma wanda duk ya sare, don ya gajiya, za a tafi, a bar shi, kuma kashegari za a kai ga nasara.

Wannan ne karo na hudu da janar Muhammadu Buhari zai tsaya takarar shugabancin kasar nan, kuma a kowace fitgowarsa bai guzurin abu biyu: da masoya da makiya, domin yakan same su bila-adadin inda duk ya nufa. A kowane lokaci makiyansa kan kirkiro sharri, su labta masa; sukan kago karairayin da ba su da tushe, balle makama, su jingina masa, amma duk a banza, jama’a na tare da shi, sai dai idan bai fito ba, ko kuma ranar jefa kuri’a ba ta zo ba. A lokacin ne sukan kokarta don nuna masa halasci, su zurara masa zunzurutun kuri’un da ba wani dan siyasan da zai same su ba tare da wata munakisa ba.
A wannan karon sai ga shi nan ana ta kitsa wasu maganganu don muzgunawa gwarzon jama’a, Janar Buhari: Wai idan da ya san dadin kujerar mulkin dimokuradiyya har yake ta dagewa don darewa bisanta me ya kai shi hambarar da Shugaba Shehu Shagari daga kanta a shekarar 1983? E, to, Janar Buhari ya zama shugaban gwamnatin mulkin soja bayan an hambarar da Shehu Shagari, amma ba shi da hannu cikin aika-aikar dakushe dimokuradiyya a wancan karon. Haka nan kuma dagewar da Janar Buhari ke yi don gurfana gaban alkalai a dukkan lokuta da aka kammala zabe ba, domin biye son zuciyarsa ne ba, sai dai don karfafa dimokuradiyya, kuma hakan ne sanadiyyar inganta hanyoyin gudanar da siyasa da al’amuran zaben a kasar nan.
Idan aka komo zargin da ake masa na hambarar da gwamnatin dimokuradiyya sai a ce ai wadanda suka ci amanar kasarsu ne bayan sun yi rantsuwar kare muttuncinta suka hamabarar da Shagari, suka kuma gayyato Janar Muhammadu Buhari, suka dora shi bisa mulki, don sun san ba shi da wani tabo, kuma ba shi da wani abin fada, kowa zai amince da shi. To amma bisa ga wata boyayyiyar manufa ce suka yi haka. Sun jira har zuwa lokacin fitar da maitarsu a fili ya zo sa’annan suka wancakalar da shi don aiwatar da mummunar manufarsu, kuma hakan aka yi.
To ai su wadancan din da suka hambarar da Buhari suka ruguza dukkan tsare-tsaren da ya yi don taimaka wa kasar nan kai wa ga kasaita, suka kuma bullo da wasu manufofin da suka bayar da damar daurewa Yahudu da Nasara Najeriya inda suke bukata, aka yi ta tatsa. Baicin haka nan kuma su ne suka yi sanadiyyar wanzuwar yanayin da ya haifar da dukkan matsalolin da kasar ke fama da su a halin yanzu, suka kuma dauki matakan ruguza yankin Arewacin kasar nan don neman gindin zama ga ‘yan Kudun da ba su kaunarsu, ba su kuma son ci gabanta. Idan da a ce sun bar Buhari bisa mulki ya dan jima ai da yanzu Najeriya ta yi kunnen dokin da kasashen nahiyar Asiya, wadanda ake mamakin ingantuwar arzikinsu cikin dan kankanin lokaci, saboda da kyakkyawan shugabancin da suka samu.
Su wadancan da suka hambarar da mulkin Buhari, yawancinsu duk ‘yan Arewa ne wadanda suka zame tamkar ‘ya’yan goribar da ke janyo wa uwarsu jifa, domin kuwa su ne suka gurgunta ta. Saboda salon mulkin da suka dade ne suna yi, ‘yan kudu ke ganin wallen ‘yar Arewa, har suna gorantawa, suna cewa ‘yan Arewa sun mayar da mulkin kasar nan gadon kaka-da-kakanni. Kuma a dalilin haka ne yankin Arewar ya shiga cikin mawuyacin hali, bayan wadancan makiya mulkin soja na Buharin sun taru, sun makure Arewa, sun danka wa wani dan Kudun da ya karasa gurgu da tadiye. Amma sai ga shi nan har yanzu ba su daddara ba, domin yayin da Janar Buhari ke ci gaba da kokarin dankar ragamar mulki don dawo da martabar Arewa da kuma kyautata al’amuran kasar, wadancan tsoffin shugabannin sai kara zarmewa suke yi wajen gwara kawunan ‘yan Arewa da kuma daukar matakan dakile manufofin Janar Buhari. A cikinsu wa ya taba nuna kauna ga Janar Buhari, ko taimaka wa fafutikarsa ta daukaka matsayin kasarsa? Ya dai tabbata wadancan shugabannin ne makiyan dimokuradiyya ba Janar Buhari ba.
To idan har wadancan tsoffin janarorin na sha’awar tsira da mutuncinsu sai su fito fili, su darje daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar nan, ‘yan asalin Arewa, su ba shi goyon bayan da zai kai shi ga nasara. Idan kuwa ba haka ba an san manufarsu: so suke kawunan ‘yan Arewa su ci gaba da rarrabuwa don dan kudun da suke goyon baya a fakaice ya ci gaba da mulki, ya kuma mayar da ‘yan Arewa kaskantattu, marasa galihu a kasar haihuwarsu.