Janar Muhammadu Buhari

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matsalar da yi wa wadanda ke zaune a jihohin da ba nasu na asali ba rijista za ta jawo sai tafi ta Boko Haram, saboda haka ta bayar da umarnin nan take a dakatar  da yi wa mutane rajista ko korarsu daga jihohin da suke zaune domin neman abincinsu.Gwamnati ta […]

Janar Muhammadu Buhari
Janar Muhammadu Buhari

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matsalar da yi wa wadanda ke zaune a jihohin da ba nasu na asali ba rijista za ta jawo sai tafi ta Boko Haram, saboda haka ta bayar da umarnin nan take a dakatar  da yi wa mutane rajista ko korarsu daga jihohin da suke zaune domin neman abincinsu.
Gwamnati ta bayar da wannan umarnin ne ranar litinin jim kadan bayan kammala taron Majalisar  Tsaro ta kasa da shugaba Jonathan ya jagoranta.
Majalisar tsaron ta yi nuni da cewa, yi wa ‘yan Najeriya wadanda ba ‘yan asalin jiha ba rijista ko korarsu daga jihar na iya wargaza kasar nan.
An dai gudanar da taron ne a cikin ofishin shugaban kasa, wanda daukacin shugabannin tsaron kasar nan suka halarta.
Shugaban ‘yan sanda Muhammad Abubakar ya bayyana wa manema labarai na fadar gwamnati jim kadan bayan fitowa daga taron cewa, taron ya tattauna ne game da batun tayar da kayar baya da sace ‘yan matan Chibok da kuma rijista tare da korar ‘yan Najeriya da ke zaune a jihohin da ba nasu ne na asali ba da wadansu jihohi suka yi.
Shi kuwa shugaban rundunar jami’an tsaro na farin kaya (SSS) Ita Ekpeyong cewa ya yi taron ya yi alla-wadai da rijista da korar da ake yi wa wadanda aka kira ‘baki’ a wadansu jihohi, ya ce shugaba Jonathan da kansa ya bayar da umarnin a dakatar  da yin haka ba tare da kata lokaci ba.
Ya cigaba da cewa, taron ya yi la’akari da martanin da wadansu mutane suka mayar a Kano da kuma wadansu jihohi game da lamarin, inda taron ya lura cewa al’amarin zai jawo matsalar da za ta iya wargaza kasar nan.
A cewarsa, ‘’Shugaban ‘yan sanda ya bayyana muku abin da muka tattauna a taron, inda aka tako batuttuwan yaki da Boko Haram da kokarin da gwamnati ke yi wajen ceto ‘yan matan Chibok da kuma batun rajista da korar ‘yan Najeriya da ke zaune a jihohin da ba nasu na asali ba da ake yi a wadansu jihohi, al’amarin da muke ganin matsalar da za ta jawo sai ta fi ta Boko Haram.’’ Mun dauki wannan al’amarin da muhimmaci kwarai da gaske, a ce mutane suna korar mutane daga wani wuri zuwa wani wuri, ko a yi wa wadanda ba ‘yan asalin jiha ba rajista, alhali suna da ‘yancin zama a duk inda suke so.Hasali ma dai saboda damuwa da al’amarin ne ya sanya za a gudanar da taron Majalisar kasa a mako mai zuwa domin tattauna matsalar.’’Inji shi.
Dangane da dadewar da aka yi ba a ‘yanto ‘yan matan Chibok ba kuwa, sai ya ce,’’mun san wurin da suke, amma ba mu so ne mu jefa rayuwarsu cikin hadari.’’
An dai fara yi wa ‘yan Arewa mazauna jihohin Enugu da Imo ne rijista tare dab a su kantin shaida domin tantance nagari da bara-gurbi a cikinsu, kodayake Gwamna Rochas Okorocha na Imo ya ce ba da izinin gwamnatinsa ne aka yi wa ‘yan Arewa rijista a jiharsa ba, a ganinsa, an sanya harkar siyasa a game da batun rajistar baki a jiharsa.
Cikin ‘yan kudu ya duri ruwa
Shugabannin kabilu mazauna yankin sabon gari a birnin Kano, sun koka tare da bayyana fargabarsu a game da matakin da wata kungiya ta dauka wajen ganin Majalisar dokokin  jihar  Kano ta yi dokar da za ta sanya a yi rijistar  baki ‘yan asalin kudancin kasar nan, kamar yadda  aka yi a wadansu jihohi na yankin kudu maso gabas ga ‘yan asalin arewacin Najeriya.
Haka nan kuma wata kungiya ta matasan Arewa ta fitar da wata sanarwa inda ta bai wa bakin kabilun na kudancin Najeriya mazauna Kano wa’adin makonni biyu da su bar jihar, a sakamkon bambancin da suka ce ‘yan uwansu na jihohin kudu suke nuna wa ‘yan asalin Arewa mazauna jihohin nasu.
Shugabannin kabilun da suka hada da na Ibo da na Yarabawa da na kudu maso kudu, sun nuna damuwarsu da rashin amincewa da wannan matakin da kungiyoyin na Arewa suka dauka.
A wata sanarwa da suka fitar sun bayyana cewa, “mun damu kwarai da kalaman da kungiyar matasan Arewa ta NYDF ta rubuta wanda ta mika wa Mai martaba Sarkin Kano  tana bukatar duk kabilu ‘yan kudancin kasar nan su tashi daga yankin Arewa nan da makonni biyu don maye gurbinsu da ‘yan Arewa da za su dawo gida daga kudanci.”
Shugabannin kabilun sai suka bukaci gwamnatin tarayya ta gagguta daukar matakin bincikawa tare da dakile shirin da kungiyoyin na Arewa suke yi, wanda suka ce ba zai haifar da da mai ido ga dorewar Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa ba. Haka nan kuma sun yi kira ga gwamnonin Arewa da kada su saurari kalaman wadannan kungiyoyin.
Haka kuma shugabannin bakin kabilun sun kai wa Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II ziyara tare da bayyana masa damuwarsu, inda suka bukaci ya yi amfani da matsayinsa na uban kasa ya hana daukar wannan matakin.
Sun kuma kai irin wannan ziyarar ga shugaban Majalisar dattawan Arewa (NEF), danmasanin Kano, Alhaji Dokta Yusuf Maitama Sule, wanda shi ma suka bayyana masa damuwarsu.
Da haka lamarin Boko Haram ya fara   -Eze Bonaface
A tattaunawarsa da Aminiya, shugaban Inyamurai mazauna Kano, Cif Eze Bonaface Ibekwe, ya ce “mun je wajen Sarkin Kano ne don mu bayyana damuwarmu game da wani labari a kan ziyarar da wata kungiya ta matasan Arewa ta kai wa Sarkin tare da fitar da wata sanarwa inda ta ba mu makonni biyu mu bar Kano kuma ‘yan Arewa mazauna kudu za su dawo gida.”
Ya ci gaba da cewa,  “abin da ya sa suka damu saboda haka al’amarin Boko Haram ya fara kamar wasa, yanzu har ya zama abin da ya zama. Ya ce sun gamsu da karkar da Sarkin Kano ya yi musu tare da jawabansa na kwantar da hankali, inda ya tabbatar da cewa babu abin da zai faru na tashinsu daga Kano. Ya ce, “rijistar da ake yi wa ‘yan Arewa a kudancin Najeriya ba gwamnatocin jihohin ne suka sa a yi hakan ba, su shugabannin ‘yan arewa mazauna kudun ne suke yin rijistar sunayen don daukar matakin tsaro.”
Ba domin raba kasa muke son yi wa ‘yan kudu rijista ba – Bulama Bukarti

Shi kuwa shugaban kungiyar  ‘yan kishin Arewa, Barista Bulama Bukarti, a hirarsa da Aminiya cewa ya yi, su ba sa ganin wannan matakin nasu zai kawo rabuwar Najeriya, domin kuwa sun dauki matakin ne don inganta tsaro a yankin Arewa.
Ya ce “kowa ya san laifuffukan da ‘yan kudu suke aikatawa, irin su fashi da makami da garkuwa da mutane da kuma kafa masana’antar samar da jariran domin sayarwa. Muna so a yi musu rijista ne don mu kare Arewa, kada su kawo mana irin wadannan laifukan jihohinmu.”
Ya yi nuni da cewa, wannan matakin nasu ba ramuwar gayya ce ga abin da ake yi wa ‘yan Arewa a kudu ba, sai dai matakin kariya ne suke dauka. Ya ce, “idan dai abin da suke yi wa ‘yan Arewa a kudu daidai ne, to muma abin da muke so a yi daidai ne.”
Ya ce tun da suka dauki matakin ba su samu koke ko kalubale ba, sai ma yabo ake tura musu ta waya a game da matakin nasu.