Janar Rabe Abubakar ya rasu a hannun ’yan bindiga

Gwamnatin Katsina ta sanar da rasuwar Manjo-Janar Rabe Abubakar (Ritaya) a hannun ’yan bindiga da suka yi garkuwa shi a jihar.

Janar Rabe Abubakar ya rasu a hannun ’yan bindiga

Rabe Abubakar

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rasuwar Manjo-Janar Rabe Abubakar (Ritaya) a hannun ’yan bindiga da suka yi garkuwa shi a jihar.

Kwamishinan Harkokin Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Katsina, Dakta Nasiru Mu’azu, ya sanar a ranar Asabar cewa Manjo-Janar Rabe Abubakar ya rasu ne yayin da yake tsare a hannun ’yan bindiga, duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar da hukumomin tsaro suka yi na tabbatar da an kuɓutar da shi.

Sanarwar ta bayyana cewa marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka haɗa da ciwon sukari da hawan jini, tana mai bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Gwamnatin ta nuna matuƙar alhini kan lamarin, tana mai cewa sace marigayin da kuma rasuwarsa daga bisani babban rashi ne ba ga iyalansa da jihar Katsina kaɗai ba, har ma ga Nijeriya baki ɗaya.

 

Yadda Janar Rabe ya shiga hannun ’yan bindiga

Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da Manjo-Janar Rabe Abubakar tare da matarsa ne a yayin da ma’auratan ke hanyarsu ta zuwa mahaifarsa da ke Batsari a Jihar Katsina.

Shaidu a yankin sun bayyana cewa ’yan ta’adda sun fito daga daki ne suka tare hanyar sannan suka buɗe wa motar wuta, dole ta tsaya.

Sun bayyana cewa maharan sun harbi direban motar amma daga baya suka ƙyale shi, suka tafi da ma’auratan.

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce yadda aka aiwatar da harin ya nuna alamar ’yan ta’addan sun yi ta bibiyar motsin Janar ɗin tun daga Kaduna kafin a ƙarshe su bude wa motarsa wuta.

Daga bisani wani jagoran ’yan bindiga da ya tayar da tuba, Kachallla Muhammadu Fulani, ya tuntuɓi ’yan uwan tsohon Janar ɗin tare da fitar da bidiyon ma’auratan a hannunsa.

A cikin bidiyon matar Janar Rabe ta bayyana sharadin da Kachallla Muhammadu Fulani ya bayar na sakin wasu mutanensa uku da kuma dabbobinsa da gwamnati ta kama, kafin ya saki ma’auratan — buƙatar da tun da farko ya bayyana wa dangin marigayin.

A nasa jawabin, marigayin ya ce ’yan ta’addan sun bayyana shirinsu na komawa yin sulhu da zaman lafiya ba tare da yaudara ba, yana mai bayyana muhimmancin zaman lafiya a yankin.

Da farko Fulani ya yi alƙawarin sakin matar, amma ya fasa, bisa hujjar cewa an girke jami’an tsaro a yankin Batsari, waɗanda da ya sake ta da sun yi iƙirarin cewa su ne suka ceto ta.

 

Ta’aziyyar Rasuwar Janar Rabe Abubakar

A saƙon ta’aziyyarsa, sanarwar, Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana lamarin a matsayin wani baƙin al’amari da ke nuna irin ƙalubalen tsaro da al’ummomi ke fuskanta a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Gwamnan ya ce wannan al’amari ya sake jaddada muhimmancin haɗa kai da ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ’yan bindiga da sauran nau’o’in aikata laifuffuka da ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Haka kuma, ya sake nanata aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an gurfanar da waɗanda ke da hannu a sace tsohon Manjo Janar Rabe Abubakar da kuma mutuwarsa a gaban kuliya.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnan ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnati na ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da matsalar ’yan bindiga tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.