Janar Swaka ya kafa sabuwar kungiyar ’yan tawaye a Sudan ta Kudu
Tsohon Janar din sojan Sudan ta Kudu da ya yi murabus a watan jiya ya fadi a ranar Litinin da ta gabata cewa ya kafa wata kungiyar ’yan tawaye da za ta kaddamar da yaki da Shugaban kasar Salba Kiir.Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa Laftana Janar Thomas Cirillo Swaka, wanda a baya […]
Tsohon Janar din sojan Sudan ta Kudu da ya yi murabus a watan jiya ya fadi a ranar Litinin da ta gabata cewa ya kafa wata kungiyar ’yan tawaye da za ta kaddamar da yaki da Shugaban kasar Salba Kiir.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa Laftana Janar Thomas Cirillo Swaka, wanda a baya shi ne tsohon mataimakin hafsa mai kula da samar da kayayyaki da dabarun yaki, ya yi murabus ne bayan da ya zargi Shugaba Kirr da mayar da sojojin kasar zuwa “sojin kabila.”
Ya ce, an fi daukar ’yan kabilar Dinka ta Shugaba Kirr a aikin soja da ’yan sanda da sauran sassan.
Janar Swaka yana daga cikin manya hafsoshi uku da suka yi murabus a watan Fabrairu ka zargin kabilanci da fifita dangi da cin hanci da rashawa da sauran barna a gwamnatin Kiir.
Sanarwar da ya fitar a ranar Litinin Janar Swaka ya ce sunan sabuwar kungiyar ’yan tawayen shi ne kungiyar Ceton kasa, (National Salbation Front -NSF), kuma “ta gamsu cewa muddin ana son dawo da kasar cikin hayyacinta tare da samun zaman lafiya tilas ne Shugaba Kiir ya barkujerar mulki.”
Sudan ta Kudu mai albarkatun man fetur, kasa ta baya-bayan nan da ta samu ’yancin kanta ta tsunduma cikin Yakin Basasa ne a shekarar 2013 bayan da Shugaba Kiir ya kori mataimakinsa kuma babban abokin hamayyar siyasarsa, Riek Machar.
An shawo kan tashin hankalin bayan kulla wata yarjejeniya a shekarar 2015, kuma Machar, wanda ya bar Juba babban birnin kasar ya koma a watan Afrilun bara inda aka sake mayar da shi kan mukaminsa.
Sai dai rikicin kabilanci da ke tsakanin mutanen biyu ya jawo daukar makami a tsakanin sojojin kasar a watan Yulin bara a birnin Juba, inda yaki ya ci gaba da fadada zuwa sassan kasar nan.
Machar yanzu na zaune ne a kasar Afirka ta Kudu bayan ya gudu daga Sudan ta Kudu lokacin da rikicin ya barke.
Sabuwar kungiyar ’yan tawayen za ta iya dada jefa kasar a cikin rikici, wadda dama rikicin ya watsu a sassanta tare da raba mutum miliyan uku da muhallinsu, lamarin da ya jawo nakasu ga harkokin noma da dada jawo talauci a kasar, wadda tuni aka ayyana cewa ynuwa ta mamayi wasu sassanta.
Kakakin Sojin kasa, Birgediya Janar Lul Ruai Koang, ya shaida wa Reuters ba zai ce komai yanzu ba game da kafa sabuwar kungiyar ’yan tawayen, sai ya samu lokaci ya karanta sanarwar Swaka.