Janar Tsiga ya shafe kwanaki 40 a hannun masu garkuwa duk da biyan kuɗin fansa
Da farko waɗanda suka yi garkuwa da tsohon Janar ɗin, sun buƙaci a ba su naira miliyan 250

Bayan shafe kwanaki 40 har yanzu waɗanda suka yi garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar Kula da Masu Yi wa Ƙasa Hidima ta Najeriya (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya ba su sako shi ba duk da cewa an biya kuɗin fansa.
Rahotanni sun nuna cewar an biya maƙudan kuɗaɗe don ganin an sako Janar Tsiga, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 5 ga watan Fabrairun da ya gabata a Ƙaramar Hukumar Bakori da ke Jihar Katsina.
- Wata 11 da tuɓe rawanin wasu sarakuna a Sakkwato
- Kofin Duniya: ’Yan wasan cikin gida 8 da Super Eagles ta gayyata
Wata majiya ta kusa da iyalansa ta ce bayan kai kuɗin, sai da aka shafe mako guda kafin ’yan bindigar suka sake tuntuɓar iyalansa, inda suka haɗa su ta waya, sannan kuma suka sake neman ƙarin wasu kuɗaɗe.
“Saboda wasu dalilai gaskiya ba zan faɗi adadin kuɗin da aka biya ba amma kuɗaɗe ne masu yawan gaske,” a cewar majiyar.
Da farko dai waɗanda suka yi garkuwa da tsohon Janar ɗin, sun buƙaci a ba su naira miliyan 250 a matsayin kuɗin fansa, sai dai an ci gaba ta tattaunawa da su.
Wasu bayanai na cewa akwai yiwuwar waɗanda suka yi garkuwa da shi sun sauya masa matsugunni.
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Najeriya ACF da kuma ta Dattijan Jihar Katsina KEF, sun buƙaci gwamnatin da kuma rundunar sojojin ƙasar, su matsa ƙaimi wajen ganin an kuɓutar da shi da sauran mutanen da aka yi garkuwa tare da su.