Kasurgumin ɗan bindiga Janbros ne ya saci ɗaliban Kuriga — Majiyoyi

Ɗaya ne daga cikin manyan ’yan ta’addar da ake zargi da kashe-kashe da sace-sacen mutane a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kasurgumin ɗan bindiga Janbros ne ya saci ɗaliban Kuriga — Majiyoyi

Aƙalla majiyoyi masu tushe uku ne suka tabbatar mana cewa kasurgumin ɗan bindigar nan da aka fi sani da Yellow Janbros ne ya sace ɗaliban makarantar Kuriga.

Janbros ɗaya ne daga cikin manyan ’yan ta’addar da ake zargi da kashe-kashe da sace-sacen mutane a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Bayanai sun ce Janbros ne ya saci sama da ɗaliban firamare da karamar sakandare 130, wanda kawo yanzu 131 na hannun gwamnatin Jihar Kaduna bayan an ceto su a ƙarshe makon da ya gabata.

An kuma bayyana cewa akwai sauran ɗalibai shida da aka kwantar a asibiti domin tabbatar da ingancin lafiyarsu a karkashin kulawar sojoji.

A baya-bayan nan dai an sha bayyana cewa an kashe Janbros a artabu ko da sojoji ko kuma da ’tan kato da gora, sai daga baya ya ƙara bayyana.

Wata majiyarmu da ba ta so mu ambaci sunanta ba, ta ce, “ina tabbatar muku cewa Janbros ne ya saci yaran nan, kuma ya yi haka ne domin ya tozarta gwamnati.”

“’Yan ta’addar sun san cewa sun riga da sun talauta mutanen kauyuka, sun kwashe dabbobinsu sun fatattake su daga gonakinsu. Sun san mutanen kauyen ba su da abin da za su sayar da kuma biyan kudin fansa.”

Wata majiyar kuma ta ce, Janbros da mutanensa sun ɗauki kwanaki suna tafiya da yaran a cikin daji domin gujewa jami’an tsaro.

Har yanzu dai babu wani bayani dangane da dabarun da aka bi wurin karɓo yaran ba tare da an zubar da jini ba.

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi

Ɗan shekara 85 ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe

Yadda muke rayuwa bayan mutuwar mazajenmu —Matan sojoji