Janet Jackson da Chris Brown da 50 Cent sun cashe a Saudiyya
Fitattun mawaka da makadan Amurka sun cashe a birnin Jeddah na Saudiyya a wani biki da ’yan kasar suka dade suna jira. An gudanar da gagarumin bikin ne a Dandalin Sarki Abdallah a birnin Jedda, kuma daga cikin mawakan da suka cashe akwai Janet Jackson da 50 Cent da Chris Brown da sauransu. Wannan shi […]
Fitattun mawaka da makadan Amurka sun cashe a birnin Jeddah na Saudiyya a wani biki da ’yan kasar suka dade suna jira.
An gudanar da gagarumin bikin ne a Dandalin Sarki Abdallah a birnin Jedda, kuma daga cikin mawakan da suka cashe akwai Janet Jackson da 50 Cent da Chris Brown da sauransu.
Wannan shi ne bikin cashewa na farko da aka taba gudanarwa a kasar Saudiyya.
Dandazon ’yan kallo sun yi ta shewa cikin annashuwa da yanayi na ba-saban-ba, saboda shekara biyu da suka gabata idan aka ce za su samu dama irin haka ba za su amince ba.
Baya ga fitattun mawakan Amurka an kuma gayyato fitattun mawakan Larabawa kamar Tamir Husny da Muhammad Abdou da sauransu kamar yadda BBC ya ruwaito.
Hotunan da aka yada a kafafen sadarwa na Intanet sun nuna Janet Jackson da ayarinta sun yi shiga ba kamar yadda aka saba gani ba ta tsaraici dukkansu sanye da bakaken tufafi.
An yi cashewar ce ba tare da Nicky Minaj ba, wacce ta sauya ra’ayi bayan gayyatarta saboda damuwa da ’yancin mata da masu luwadi da madigo a Saudiyya.