Jang na kokarin sake dora dan yankinsa kan kujerar Gwamnan Filato – Nuhu Gagara

A yayin da zaben badi ke kara gabatowa, dambarwar siyasar yankin da zai fitar da dan takarar Gwamnan Jihar Filato a tsakanin shiyyoyin jihar tana kara kunno kai. A tattaunawar wakilinmu da tsohon Kwamishinan Watsa Labarai na jihar Mista Nuhu Gagara wanda ya fito daga Shiyyar Tsakiyar Jihar ya zargi Gwamna Jang wanda ya fito […]

Jang na kokarin sake dora dan yankinsa kan kujerar Gwamnan Filato – Nuhu Gagara

A yayin da zaben badi ke kara gabatowa, dambarwar siyasar yankin da zai fitar da dan takarar Gwamnan Jihar Filato a tsakanin shiyyoyin jihar tana kara kunno kai. A tattaunawar wakilinmu da tsohon Kwamishinan Watsa Labarai na jihar Mista Nuhu Gagara wanda ya fito daga Shiyyar Tsakiyar Jihar ya zargi Gwamna Jang wanda ya fito daga Arewa da kokarin sake dauko da dan takarar Gwamnan jihar daga yankinsa. To, amma mai ba Gwamnan shawara kan Harkokin Watsa Labarai, Mista Ayuba Pam ya ce a tarihin zaben Gwamna ba a taba bin tsarin karba-karba a tsakanin shiyyoyin jihar ba:

Daga Husaini Isah, Jos

Aminiya: Yaya kake kallon shirye-shiryen zaben Gwamnan Jihar Filato a badi musamman ganin Gwamna Jang ya gama wa’adinsa?
Nuhu Gagara: A gaskiya tunda Gwamna Jang yana kan wa’adinsa na karshe, mu mutanen Filato a tunaninmu ya kamata zuwa yanzu a ce an dauki hanyar da za a bi kan zaben sabon Gwamna a badi. Amma har zuwa wannan lokaci da muke magana an yi shiru, a sauran jihohin da suke makwabta da Jihar Filato harkokin siyasa suna tafiya. Za ka ga an manna fastocin masu sha’awar takara, a ko’ina ’yan siyasa suna ta kaiwa da komowa ana sanar da jama’a cewa lokaci ya gabato. Amma mu a Filato da wuya ka ba da sunayen wadanda suke sha’awar takarar kujerar Gwamnan Jihar a zaben badi. Duk da cewa Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta fitar da jadawalin zabubbukan masu zuwa. Babbar dumuwar ita ce duk wanda ya tashi ya je ya samu Gwamna Jonah Jang ya nuna masa yana son ya taimake shi zai tsaya takarar Gwamna a badi, sai abin ya zama damuwa Gwamnan ya kama fada. Kamar Gwamnan ba ya son ya ji wani ya ce zai tsaya takarar Gwamnan. Kuma ga shi lokaci ya gabato domin yanzu saura shekara daya da watanni don haka dole ne a samu wanda zai zama sabon Gwamna.
Aminiya: Me kake ganin ya kawo haka?
Nuhu Gagara: A matsayina na dan siyasa kuma dan Jihar Filato wanda ya san cikin wannan gwamnati. Ina tunanin ana yin haka ne domin a yaudari mutane, saboda idan ka je ka ce kana son ka zama Gwamna, aka yi maka tsawa za ka koma baya ka yi shiru, idan wani ya je shi ma haka za a yi masa don haka shi ma sai ya koma baya ya yi shiru. A tunaninmu ana son sai lokacin zabe ya zo gab sai a dauko wa mutanen Jihar Filato wanda bai cancanta ba a dora musu. Domin muna sane da cewa akwai wasu da suke jikin Gwamna Jang suna ta tarurruka da mutane kan za su nemi kujerar Gwamnan Jihar Filato. A bangare daya ana cewa da sauran lokaci a jira, a daya bangaren kuma an bar wasu suna gudanar da harkokin siyasa ta takara kujerar Gwamnan. Don haka muna ganin akwai rashin gaskiya kan wannan al’amari. Idan kana jin kalaman Gwamna Jang da kalaman na kusa da shi, za ka gane cewa akwai wani abu a kasa kan zaben Gwamnan Jihar a badi. Mu a Jihar Filato mun saba hada kai a yi abu tare, irin wannan hadin kai ne ya sa Gwamna Jang ya samu kujerar Gwamna. Tunda aka kafa Jihar Filato ba a taba samun Gwamna daga yankin Arewacin Jihar ba, sai a kan Jang. Kuma da kyar aka samu domin mun wahala kafin mutane su yarda. Mu mun yi haka ne saboda shiyyar Arewar tana cikin jihar ne. Tunda yankin Kudancin Jihar sun yi Gwamnan, yankin Tsakiya sun yi, to ya kamata yankin Arewa ma su yi. Yanzu lokaci ne na yankin Kudu ko Tsakiya. Amma sai ga shi wasu sun fara cewa ai adashi ne, inda aka ci a karshe nan ne za a fara sake ci.
Aminiya: Wato kuna ganin kamar Gwamna Jang yana kokarin ganin an zabo dan takarar Gwamna daga yankinsa na Arewacin Jihar ke nan?
Nuhu Gagara: Babu shakka yana kokarin yin haka, domin duk maganganun da ake cewa ba haka ba ne, mun tabbatar akwai sunayen irin wadannan mutane da suke ta yakin neman zaben Gwamnan. Wannan ya nuna cewa wadannan mutane suna daukar kujerar Gwamnan Jihar Filato ta zama kamar gadonsu. Siyasa ba ta gaji haka ba, siyasa abu ne na jama’a saboda haka a bar mutanen Filato su zabi wanda ya dace. A yanzu mutanen Filato sun san irin mutumin da ya dace wanda zai ceto jihar nan daga cikin halin da take ciki. Domin yau a Jihar Filato babu yarda da juna wanda da ba haka muke ba a da. Wannan gwamnati ta Jonah Jang da yanzu take da shekara bakwai an samu matsala a cikinta. A yau mutumin yankin Filato ta Tsakiya ba ya jin dadin mutumin yankin Arewacin Filato, a yankin Arewacin Filato ma mutanen yankin ba sa jituwa da junansu. A yanzu a Filato kowa ya san duk ayyukan raya kasa da ake yi a jihar ana yi ne a yanki daya wato yankin Arewacin jihar kuma yankin kabila daya. Sam wannan bai dace ba, domin rashin adalci ne. Mutane sun fusata da wannan rashin adalci, don haka muna addu’a tare da fatar samun wanda zai cetomu daga cikin wannan hali ya hada kan mutanen Jihar Filato.
Aminiya: To, amma a ’yan kwanakin nan Gwamna Jang ya fito yana cewa bai ba yankin Arewacin jihar damar su fito da ‘dan takarar kujerar Gwamnan Jihar ba, me za ka ce?
Nuhu Gagara: Yana iya fadar haka, amma shi da kansa yana cewa yana jiran lokacin da Allah zai fada masa wanda zai gaje shi. Ya kamata a bar abin a bude domin mulkin dimokuradiyya ake yi. Duk wanda ya zo ya same shi ya nuna masa cewa yana sha’awar ya fito takarar Gwamnan Jihar Filato ya ce masa abin na jama’a ne don haka ya je ya yi kokari ya nemi jama’a, in Allah Ya ba shi a ba shi goyon baya. Amma ba in mutum ya zo ya ce zai nemi takarar Gwamna a kama shi da fada ba. Kuma ana wannan fadan amma an san cewa a wani bangaren wasu suna ta yakin neman zabe. Al’ummar Jihar Filato ba za su amince da wannan danniya da ake son a nuna masu ba. Don haka za mu ci gaba da yin addu’a Allah Ya kawo mana wanda zai kawo mana gyara kan halin da muka shiga a jihar nan. Kuma mun gode Allah kan kokarin gyaran da ake yi a halin yanzu a uwar jam’iyyarmu ta PDP ta kasa. Yanzu sabon shugaban jam’iyyar Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu kowa ya san ya yi damara kan cewa za a yi gaskiya a harkokin wannan jam’iyya. Don haka muna kira ga Jam’iyyar PDP reshen Jihar Filato kan ta yi koyi da uwar Jam’iyyar PDP ta kasa. A kwanakin baya gwamnoninmu 5 sun fice daga cikin wannan jam’iyya saboda irin wadannan matsaloli na take hakkin mutane. Don haka ina kira ga shugabannin jam’iyyar a Jihar Filato tun daga mazabu zuwa kananan hukumomin da jiha baki daya, su tabbatar sun ba kowane dan jam’iyya hakkinsa.
Aminiya: A karshe wane sako ko kira ne kake da shi ga al’ummar Jihar Filato?
Nuhu Gagara: Ina kira ga al’ummar Jihar Filato kan idan zabe ya zo su hada kai  su dubi mutumin da ya cancanta, mai tsoron Allah ba wanda zai  tashi ya je coci ko masallaci ba, ya ce shi mai ibada ne, amma zuciyarsa ba haka take ba. Ba irinsu muke bukata ba, muna bukatar mutane ne masu tsoron Allah na gaskiya.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno