Jang ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da addu’o’in zaman lafiya

Gwamnan Jihar Filato Mista Jonah Jang ya yi kira ga ’yan Najeriya su ci gaba da yi wa kasar nan addu’o’in neman zaman lafiya. Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wajen addu’o’in bikin cikar Najeriya shekara 54 da samun mulkin kai da aka gudanar a babban masallacin Jos.Gwamnan wanda mashawarcinsa kan harkokin shari’a Alhaji […]

Jang ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da addu’o’in zaman lafiya
Jang ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da addu’o’in zaman lafiya

Gwamnan Jihar Filato Mista Jonah Jang ya yi kira ga ’yan Najeriya su ci gaba da yi wa kasar nan addu’o’in neman zaman lafiya.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wajen addu’o’in bikin cikar Najeriya shekara 54 da samun mulkin kai da aka gudanar a babban masallacin Jos.
Gwamnan wanda mashawarcinsa kan harkokin shari’a Alhaji Dauwa Lamba ya wakilta ya ce zaman lafiya shi ne ginshikin ci gaban gaban kowace kasa a duniya. Don haka ya zama wajibi ’yan Najeriya su yafe wa juna su zauna lafiya domin a samu ci gaba a kasar nan.
Gwamna Jang ya yaba wa al’ummar Jihar Filato kan gudunmawar da suka bayar wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar. “Babu shakka a baya mun yi fama da rikice-rikice a jihar nan, amma ta hanyar addu’o’i da gudunmawar da al’ummar jihar suka bayar, yanzu zaman lafiya ya dawo. Don haka ya zama wajibi mu hada kai mu ci gaba da addu’o’i don dorewar wannan zaman lafiya a jihar nan da kasa baki daya,” inji shi.
A nasa bayanin wanda ya jagoranci gudanar da addu’o’in mataimakin Babban Limamin Jos Sheikh Lawal Adam ya yi kira ga shugabannin Najeriya a matakai daban-daban su
tabbatar suna yi wa al’ummar kasar gaskiya da adalci kan amanar shugabancin da aka ba su.