Janye barazanar gamayyar kungiyoyin matasan Arewa har yanzu tana kasa tana dabo

Tun a cikin watan Yunin da ya gabata da gamayyar kungiyoyin Matasan Arewa suka ba da wa`adin 1 ga watan jibi na Oktoba in Allah Ya  kaimu ga `yan kabilar Ibo mazauna dukkan jihohin arewa 19, da ta zama ranar da za su tattatar yanasu-yanasu kaf, su bar arewa kafin waccan rana, wasu jama`a da […]

Janye barazanar gamayyar kungiyoyin matasan Arewa har yanzu tana kasa tana dabo

Tun a cikin watan Yunin da ya gabata da gamayyar kungiyoyin Matasan Arewa suka ba da wa`adin 1 ga watan jibi na Oktoba in Allah Ya  kaimu ga `yan kabilar Ibo mazauna dukkan jihohin arewa 19, da ta zama ranar da za su tattatar yanasu-yanasu kaf, su bar arewa kafin waccan rana, wasu jama`a da mahunta a kasar nan suka dukufa wajen ganin lallai sai matasan sun fito karara a bainar jama`a sun janye waccan barazana, bisa ga irin tashin-tashinar rashin zaman lafiyar da suke hasashe da zargin barazanar za ta iya haddasawa zaman lafiyar kasar nan.

Kafin wannan yunkuri wasu daga cikin masu madafun iko na Arewa, bayan sun yi tir da Allah wadai a kan wa`adin gamayyar kungiyoyin matasa, kamar Gwamnan Jihar Kaduna da kungiyoyin matasan suka yi taron ba da wa`adin a babban birnin jiharsa na Kaduna, Malam Nasiru eL-Rufa`i, har umurni ya ba jami`an tsaron kasar nan na su kama shugabannin gamayyar kungiyoyin matasan don gurfanar da su gaban shari`a. 

Daga ma can shiyyar Kudu maso Gabas  da ta kunshi jihohin Anambara da Ebonyi da Abia da Enugu da Imo, (shiyyar da ta kunshi `yan kabilar Ibon kasar nan) wasu daga ciki gwamnonisu da masu fada a jinsu, su ma sun yi kakkausar suka ga bayar da wa`adin.

Daga nan Arewa kuwa kungiyar Dattawan Arewa wato Northern Elders Forum, kadai ta hannun Kakakinta Farfesa Ango Abdullahi, ta fito ta goyi bayan wa`adin da gamayyar kungiyoyin matasan Arewan suka bayar a wancan lokacin.  

Ko shakka babu barazanar matasan dole ta zama abin damuwa matuka, musamman ga `yan kabilar Ibo da suka saki jiki suka sake baza dukiyoyinsu a dukkan lungu da sakon jihohin Arewa da ma sauran sassan kasar nan, kasancewar su ke kan gaba a cikin harkokin saye da sayarwa. Kazalika, dole `yan kabilar Ibon, musamman wadanda suke zaune a jihohin Arewa 19, su fi sauran takwarorinsu da ke sassan kasar nan damuwa, bisa ga la`akari da irin yadda suke zaune lami-lafiya a lungu da sakon Arewar. Sabanin sauran kasar nan ciki kuwa har da yankunansu na asali da suke cikin zaman kunci da hassada da kyashi. 

Wasunsu kuma musamman wadanda suka san yadda aka yi yakin basasar kasar nan har na tsawon watanni 30, tsakanin shekarar 1967 zuwa watan Janairun 1970, yakin da madugun `yan tawaye, kuma tsohon gwamnan mulkin soja na farko a tsohon lardin gabashin kasar nan, wato marigayi Kanar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu ya jefa su ciki, bayan ya bayyana kafa kasar Biafara. Yakin  da ya yi sanadiyar halaka mutane kusan miliyan daya, baya ga wadanda suka jikkata da kuma asarar dukiyoyi da kaddarori. Ko kusa bana jin masu hankalin cikinsu za su yi fatan a ce sun sake shiga cikin waccan akuba.

Zuwa yanzu wasu jama`a da mahukunta sun shiga kokarin ganin yadda za su shawo kan gamayyar kungiyoyin matasan Arewa don su janye waccan barazana. Cikin neman tabbatuwar hakan ne ta sanya tsohon mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta NLC Kwamared Isah Tijjani a ranar Laraba 4-9-17, ya shirya wani taron da ya hada da shugabannin gamayyar kungiyoyin matasan Arewa da na takwarorinsu na `yan kabilar Ibo a Kano. 

A wancan taro, shugaban gamayyar kungiyoyin matasan Arewan Shettima Yarima, ya fadi cewa sun bayar da wa`adin ne bisa ga la`akari da irin munanan kalaman cin zarafi da batunci ga shugabannin Arewa da shugaban kungiyar `yan asalin kasar Biafara Mista Nnamdi Kanu IPOB yake ta yi ba kwaba daga shugabannin shiyyar ta Kudu maso Gabas.

Shettima ya ci gaba da cewa “Kanu yana ta la`antar shugabanninmu tun tsawon lokaci da sunan neman kafa kasar Biafara, kuma ba wani daga cikin shugabannin `yan kabilar Ibo da ya taba kwabarsa. Mun fahimci abin yana neman wuce Makadi da rawa, shi ya sa muka ba da wancan wa`adi ga `yan kabilar Ibo da su fice su bar Arewa baki daya ko ma samu zaman lafiya.” In ji Shettima. 

Shi ma da yake na sa jawabi ga mahalarta taron na Kano, shugaban Majalisar Wakilan `yan kabilar Ibo mazauna jihohin Arewa 19, Cif Chi Nwogu, wanda ya la`anci kalamai da take-taken Mista Kanu da `yan kanzaginsa, yana mai cewa `yan kabilar Ibo mazauna Arewa ba su taba goyon bayan kiraye-kirayen Mista Kanu ba. Ya ci gaba da cewa “Ba za mu bar Arewa ba, inda muka girma har muka haifi `ya`ya, muke kuma kasuwancinmu, gwamma mu tattauna, don samo mafita,” inji Cif Nwogu a wajen wancan taro na Kano an kafa wani Kwamiti mai wakilai goma da ya kunshi wakilai biyar-biyar daga kowane bangare don ci gaba da nemo mafita.

Shi ma Gwamnan Jihar Borno, kuma shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa a madadin gwamnonin Arewa ya yi taro har karo uku da shugabannin gamayyar kungiyoyin matasan Arewar a Abuja da Kaduna da Maiduguri duk da aniyar ganin ya shawo kan shugabannin matasan, don su janye ikirarin bazaranar wa`adin da suka ba `ya kabilar ta Ibon. Gwamna Shettima ya fadi cewa bayar da wa`adi, zai iya sa wasu zama zauna gari banza su yi amfani da karewar wa`adin su far wa `yan kabilar Ibo mazauna Arewa, al`amarin da Gwamna Shettima  ya ce ka iya haddasa `yan kabilar Ibo su yi ramuwar gayya ga `yan Arewa mazauna Kudu maso Gabas. Ramuwar gayyar da ka iya zama sanadiyar barkewar mummunan rikici a kasar nan.

Ana cikin wannan lalube ne sai kuma ga wata waka da wata Zabiya mai jin Hausa ta wallafa ta kuma saki ta kafofin sada zumunta, wakar da aka ce ta kunshi miyagun kalaman batanci ga kulliyar `yan kabilar Ibo. Duk da jami`an tsaro sun ba da tabbacin bin sawun wadda ta yi wakar da wadanda suka sa ta, da aniyar ganin an hukunta su, amma da alama shugaban babbar kungiyar `yan kabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo, na kasa baki daya Cif Nnia Nwodo, bai ji dadin waccan waka ba.

 A wani taron manema labarai da ya kira, Cif Nwodo ya koka a kan irin yadda jami`an tsaron kasar nan suka ki kama shugabannin gamayyar kungiyoyin matasan Arewa da suka fara ba da wancan wa`adi, ya ce maimakon ma a kama su sai ganinsu ake suna ta tarurruka da wasu gwamnoni da fadi a ji na Arewar da ya kamata a ce sun kwabe su.

Mai yiwuwa Cif Nwodo ya manta da irin yadda kungiyoyinsu na MASSOB da IPOB, tsawon shekaru su na ta haniyar rashin mutunci ga shugabannin Arewa, Mista Kanu ma har gidan Radiyo ya kafa a kasar waje, inda yake da zama da yake baza  yekuwar kafa kasar Biafara da cin zarafin akasarin shugabannin arewa, amma shugabannin kungiyar Ndigbo ba su damu ba, balle su tsawata wa `ya`yan nasu ba, sai yanzu da suka ga al`amarin ya dauki wani sabon salo da gamayyar kungiyoyin matasan Arewa suka fara mayar da martini. 

Ya kamata shugabanni da mabiya na kowane sashen kasar nan, su kwan da sanin cewa haduwarmu a zaman kasa daya, zama ne na cudanni in cudeka da kowa ke bukatar kowa. Kar su bari a furta munanan kalaman kiyayya da batanci, ko da ba su kaimu ga sake yin yaki ba (Allah Ya tsare), su kaimu ga irin rikicin `yan Hutu da Tutsu na kasar Ruwanda.