Janye sojoji ya taimaka wajen harin makarantar Dapchi-Gwamnan Yobe

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce janye sojoji da aka yi ya taimaka wajen samun nasara a harin da aka kai makarantar Dapchi na Jihar Yobe. Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a lokacin da ya karbi bakuncin takwaransa kuma Shugaban Gwamnonin Arewa Alhaji Kashim Shettima a lokacin da ya zo masa jaje, […]

Janye sojoji ya taimaka wajen harin makarantar Dapchi-Gwamnan Yobe

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce janye sojoji da aka yi ya taimaka wajen samun nasara a harin da aka kai makarantar Dapchi na Jihar Yobe.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a lokacin da ya karbi bakuncin takwaransa kuma Shugaban Gwamnonin Arewa Alhaji Kashim Shettima a lokacin da ya zo masa jaje, inda ya ce sojoji ba su ma ko sanar da su cewa za su cire sojojin ba.

“ina fada da babbar murya cewa lokacin da aka kawo wannan hari babu sojoji a Dapchi domin bamu san cewa ma sun cire sojojin ba.

“da harin Dapchi da na Boni Yadi sun yi kama da juna domin duk sun auku ne ‘yan makonnin kadan bayan an janye sojoji daga yankin,” inji gwamnan.