Janye tallafi: ‘Tinubu ya fara saka da mummunan zare’

Muna ba da hakuri bisa takurar da wannan sauyin zai haifar.

Janye tallafi: ‘Tinubu ya fara saka da mummunan zare’

Shugaba Bola Tinubu

J im kadan da rantsar da sabon Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana janye tallafin man fetur, wanda hakan ya jefa kasar a cikin wani mawuyacin hali na karancin man fetur da tsadarsa.

Kuma hakan ya sa jama’a da dama zargin cewa sabon Shugaban Kasar ya fara saka da mummunan zare.

Akasarin masu sharhi da masana sun ce bai kamata Shugaba Tinubu ya furta wannan kalami a daidai lokacin da aka rantsar da shi ba, ganin cewa ba a yi wani tanadi na saukaka wa mutane ba kamar yadda gwamnatin da ya gada ta yi alkawari.

Shugaban yana bayyana janye tallafin sai gidajen mai suka rurrufe wanda hakan ya sa farashin man ya yi tashin gwauron zabo, kuma washegari farashin lita daya na man ya haura zuwa Naira 700 a wasu wurare, yayin da ’yan bumburutu suka yi ta cin karensu ba babbaka.

A jawabin Shugaba Tinubu na karbar mulki a ranar Litinin, ya ce, “Muna yaba wa gwamnatin baya kan janye tallafin mai wanda ke kara azurta wasu tsirarin mutane.”

Tuni wasu suka fara ce-ce-ku-ce, musamman masu adawa da gwamnatin APC, inda suka fara cewa tun yanzu an fara shiga wahala.

Yadda yake a jihohi

A Jihar Legas, wakilin Aminiya ya zaga, inda ya gano cewa yawancin gidajen mai duk sun rufe, sannan ’yan kadan da suke aiki, akwai dogon layi.

Wannan ya sa farashin man ya tashi matuka, wanda hakan ya jawo tsadar sufuri da karancin ababen hawa a fadin jihar.

Wani mazaunin Legas da ya zanta da Aminiya, ya yi korafin cewa ya kashe Naira 1,500 daga Iyana Ipaja zuwa Arepo maimakon Naira 700 da ya saba.

Gidajen mai a tsakiyar birnin tuni suka kara farashi, inda yawanci suke sayar da litar man daga Naira 500 zuwa 600, musamman a kan Titin Mil 2 zuwa Badagry da wakilin Aminiya ya bi.

Sai dai Aminiya ta ga wasu gidajen man NNPC da suke sayar da man a kan Naira 180, amma yawancin irinsu, ta same su a kulle.

Sai dai Aminiya ta ga wasu gidajen man da suke ci gaba da sayar da man a kan Naira 195, amma sai dai akwai dogon layi.

A Birnin Tarayya Abuja kuwa, yawancin gidajen mai sun rufe, wasu kuma suna sayar da man, amma layi ya yi yawa.

Wakilinmu da ya zagaya Kubwa da Kado da Jabi, ya ga ’yan gidajen man da suke aiki sun cika makil a ranar Talata.

Wani mai suna Stephen Ojunta ya ce, “Na je kusan gidajen mai 6 ke nan, amma ban samu mai ba domin duk sun rufe. Na je Dutse da Kado da Jahi duk ban samu mai ba.”

Sai dai Aminiya ta lura wasu gidajen man suna budewa su sayar da man, amma zuwa shekaranjiya Laraba akasarin gidajen man sun kara kudin litar man zuwa sama da Naira 500 a Abuja.

A Jihar Bauchi kuwa, wani mai suna Sani Umar cewa ya yi Shugaba Tinubu ya yi kuskuren fitar da wannan sanarwa a wannan lokaci ba tare da daukar wani mataki ba, musamman a kan masu gidajen mai.

Mutanen jihar sun koka kan yadda daga jin jawabin masu gidajen man suka kara farashinsa duk da cewa sun sayar da shi Naira 220 a ranar Lahadi da kuma safiyar Litinin din.

Dole mu cire tallafi, ko ya durkusar da kasa — Shettima

Da yake amsa tambayoyin manema labarai a Fadar Shugaban Kasa a ranar da ya kama aiki, Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima ya ce ya zama tilas a janye tallafin man, idan ba haka ba, tallafin man ne zai durkusar da kasar nan.

Ya ce, “Shugaban Kasa ya riga ya yi sanarwa game da cire tallafin. Maganar gaskiya ita ce ko dai mu cire tallafin ko kuma ya durkusar da kasarmu.

“A shekarar 2022, mu kashe Dala biliyan 10 kan kudin tallafi da yake amfanar wasu tsirarin mutane masu dukiya da suke kara azurta kansu, domin masu karfi ne suke amfana da tallafin.

“Talakawa ba wani amfana suke da shi ba. Mun san za mu fuskanci matsala daga masu cin moriyar tallafin, amma a shirye muke domin duk inda aka samu niyya mai kyau, za a samu mafita,” in ji shi.

Muna bin gwamnati bashin Naira tiriliyan 2.8 na tallafin — NNPCL

A bangaren Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL), ya ce yana bin Gwamnatin Tarayya bashin da ya kai Naira tiriliyan 2.8 na tallafin man fetur da ba ta biya ba.

Shugaban Kamfanin NNPCL, Malam Mele Kyari ne ya sanar da haka ranar Talatar da ta gabata, yayin da yake zantawa da manema labarai haka, bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a fadarsa.

Malam Mele Kyari ya ce sun yi maraba da matakin da Shugaba Tinubu ya dauka a jawabinsa na karbar mulki kan janye tallafin man fetur, inda ya ce ci gaba da bayar da tallafin ba abu ne mai dorewa ba.

Ya ce dimbin kudaden da ake kashewa sun sa kamfanin ba ya iya gudanar da ainihin ayyukan da suke kansa.

Mele Kyari ya ce ba su yi mamakin ganin dogayen layukan da suka sake bulla a gidajen mai ba, tun ranar Litinin, saboda dillalan man za su so samun karin bayani kan kalaman Shugaban Kasa cewa “Zamanin biyan tallafin mai ya wuce.”

Sai dai ya ce gwamnati za ta fito da matakan rage radadin da janye tallafin ga mutane.

Ya ce, “Bayan Naira tiriliyan shida da aka biya a 2022 da Naira tiriliyan 3.7 a 2023, ba mu karbi kowane irin tallafi daga gwamnati ba.

“Hakan na nufin tun da gwamnati ta ki biyan wadancan kudade, mu ne muka ci gaba da biya daga aljihunmu.

“Idan kudaden suka taru suka yi yawa, fargabarmu ita ce hakan zai gurgunta ayyukanmu a matsayin kamfani.

“Yanzu haka muna jira su biya mu wannan bashin na Naira tiriliyan 2.8, saboda ba za mu iya ci gaba da wannan aiki ba,” in ji Kyari.

Muna da wadataccen mai — NNPCL

A daidai lokacin da aka fara dogon layi a gidajen mai a sassan Najeriya sakamakon bayyana cire tallafin man, Kamfanin NNPC ya ce jama’a su daina fargaba akwai wadataccen mai a kasa da zai wadatar da kasar nan.

Shugaban Kamfanin, Malam Mele Kyari, ya bayyana haka a zantawarsa da BBC, inda ya ce akwai mai a ma’adanarsu, don haka babu wata matsala da yake gani za a iya fuskanta da ta shafi karancin mai.

“Dama duk lokacin da aka samu irin wannan jawabi daga shugabanni, sai mutane su yi ta tururuwa zuwa gidajen mai suna sayen mai fiye da wanda suke bukata saboda suna tsoro kada a kara kudin man,” in ji Kyari.

Ya ce bai ga abin tsoro ba domin akwai mai sosai a ajiye. Dangane da batun cire tallafin man kuwa, shugaban na NNPC, ya ce dama tallafin ya jima da zame wa NNPC matsala.

“Abin da Shugaban Kasa ya yi ya zo daidai da dokar kasa, domin matakin ya dace sosai.”

Za mu tabbatar farashin bai wuce kima ba —NMDPRA

A jawabin Shugaban Hukumar Sa-ido Kan Gidajen Mai ta Najeriya (NMDPRA), Malam Faruk Ahmed, ya bukaci ’yan Najeriya su kwantar da hankalinsu.

A jawabinsa jim kadan bayan an fara fargabar shiga matsanancin rashin mai, ya ce za su tabbatar farashin man bai wuce kima ba.

A bayaninsa da ya fitar ta hannun Janar Manajan Harkokin Watsa Labarai na Hukumar, Kimchi Apollo, ya ce hukumar tana aiki tare da NNPC da sauran masu ruwa-datsaki don tabbatar doka da oda.

Ba a fahimci bayanin Tinubu ba ne —Keyamo

Da yake karin haske kan batun, tsohon Minista a Ma’aikatar Kwadago, Festus Keyamo ya ce ba Shugaba Bola Tinubu ba ne ya cire tallafin man fetur ba.

Keyamo ya ce, kasafin kudin da Tinubu ya gada daga Gwamnatin Buhari ne bai yi tanadin biyan tallafin man ba.

Keyamo ya wallafa a Twitter cewa: “Wasu ’yan jarida ba su fahimci jawabin Tinubu ba. Kuskure ne su ce Gwamnatin Tibubu ce ta cire tallafin mai.

“Gwamnatin dai ta gaji kasafin 2023 wanda babu tanadin tallafi mai a ciki. Shugaba Tinubu ya amince da wannan yanayin ne kawai a jawabinsa na farko a dandalin Eagle Square.

“Don haka duk wani mai neman tallafin ya kamata ya gamsar da ’yan Najeriya dalilin da ya sa Shugaba Tinubu zai fara da rashin bin doka ta hanyar yin alkawarin dawo da wani abu da doka ta cire.

“Wadanda suke da’awar kare hakki ko jin dadin ma’aikata, ya kamata su gamsar da ’yan Najeriya cewa Dala biliyan 10 da ake kashewa ba ta kawo koma-baya ga tattalin arzikin kasa.

“Wannan ita ce tattaunawar da ’yan Najeriya ya kamata su shirya yi yanzu,” in ji shi.

Za mu sa kafar wando daya da gwamnati —NLC

Sai dai jim kadan bayan sanarwar ce Jam’iyyar LP da Kungiyar Kwadago da wasu kungiyoyi da jam’iyyun siyasa suka yi tir da matakin a wani lamari na farkon saka kafar wando daya da sabuwar gwamnatin Tinubu.

Kakakin Jam’iyyar na riko, Obiora Ifoh ne ya sanar da haka a madadin shugaban jam’iyyar, inda ya ce daga sanarwar ta Shugaban har an jefa mutane cikin wahala, inda a cewarsa farashin mai ya kai Naira 600 zuwa 750.

“Tuni kudin mota ya tashi a fadin kasa, sannan har an bude wa ’yan bumburuta kasuwa. Wannan wacce irin hanya ce ta sanar da zuwan sabon Shugaba?”

A ranar Laraba ce Shugaban Kasa da Kungiyar Kwadago suka zauna don tattauna batun. Mista Ajaero ya ce tun farko kamata ya yi a ce Shugaba Tinubu ya nemi sanin illa ko abin da zai iya biyo bayan cire tallafin ga talakawan Najeriya kafin ya furta magana a kai.

Ya ce matsayin NLC a bayyane yake cewa idan har Shugaban yana da kyakkyawar niyya game da lamarin, to kamata ya yi a ce an samar da wata madogara da ’yan kasa za su karkata gare ta idan aka cire tallafin.

Shugaban NLC din ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da ya ce kamata ya yi gwamnati ta yi kafin ta ambaci batun cire tallafin.

Abubuwan sun hada da gyara matatun mai hudu da samar da kyakkyawan tsarin sufuri ga ma’aikata da sauran tanade-tanade.

Abin da ya kamata a yi — Masana

Wani masanin tattalin arziki, Taiwo Oyedele ya ce akwai bukatar gwamnatin Tinubu ta zauna da masu ruwa-da-tsaki domin tattauna yadda za a biyo wa lamarin.

Oyedele ya ce bai yi tunanin Tinubu zai cire tallafin kai-tsaye kuma nan take ba, inda ya ce ya yi tunanin za a dauki akalla makonni ana shirye-shirye aiwatar da umarnin na Shugaban Kasa.

Sharhi: Bayani dalla-dalla kan tallafin mai Abin da ake nufi da tallafin mai shi ne kudin da ake biya domin rage farashin man fetur da mutanen kasa suke saya, inda gwamnati take biyan sauran kudin daga farashin da ya kamata a rika sayarwa domin rage radadi.

Ba a man fetur kadai ake biyan tallafi ba, sai dai an fi amfani da man ne.

A dalla-dalla kamar a ce mutum yana sayen gawayin girki Naira 100 ne. Sai ya kasance babu gawayin, sai an sayo daga wani waje mai nisa an kawo inda ake bukata.

To a nan sai farashin ya koma misalin Naira 200 saboda kudin dako. To maimakon mutum ya saya a Naira 200, sai gwamnati ta dauke biyan Naira 100 daga lalitarta, mutane su ci gaba da biyan Naira 100.

Haka ake lissafin kudin da gwamnati take cirewa daga lalitarta a kan duk litar mai da ake sha, wanda hakan ya sa kudin ke da yawan gaske.

Farashin man

A bara Shugaban NNPC, Mele Kyari ya ce farashin mai a can inda ake dakonsa zuwa gidajen mai ya kai Naira 510.

Wannan na nufin a farashin mai Naira 195 a kowace lita, gwamnati na cika wa mutane Naira 315 a matsayin tallafi a kowace lita.

A bana kadai an kasafta Naira tiriliyan 3 da za a kashe wajen biyan kudin tallafi zuwa watan Yuni da muka shiga da gwamnatin da ta gabata ta ce za ta biya.

Gwamnatin baya ba ta kasafta kudin tallafin ba daga watan Yuni, wanda ya zo daidai da watan da Shugaba Tinubu yake fara mulki.

Ke nan idan aka cire tallafin, akalla farashin man zai kama ne daga Naira 510 zuwa sama, wanda zai danganta ne da kudin da kowane gidan mai ya kashe wajen dakon man.

Kuma za a iya samun bambancin farashi a gidajen mai da jihohi bisa la’akari da nisansu.

An wayi garin Laraba farashin litar fetur ya kai Naira 560 a gidajen mai a Kano.

An kuma samu samu dogayen layuka a gidajen man da Aminiya ta ziyarta a Kano, inda farashin lita ke kaiwa farawa daga Naira 350 zuwa 560.

Aminiya ta je gidan mai na AYM Shafa, inda ake sayar da lita a kan Naira 560, gidan man Alhaji Alasan de ke Titin Gaida a Karamar Hukumar Kumbotso na sayarwa Naira 450; A.Y. Maikifi kuma Naira 400, maimakon Naira 220 da aka sayar a safiyar Talata.

Platinum Oil Services, na sayarwa Naira 380, sai B.A Bello, kuma Naira 350, a yayin da Kanawa ke bayyana damuwa kan tashin gwauron zabin man da kuma dogayen layin da ake fama da shi a gidajen mai.

Wani mazaunin Kano, B.A. Haruna Ishak, ya bayyana damuwa kan yadda gwamnatin ta shigo, inda ya ce ko a ranar Talata ya sayi lita a kan Naira 210, amma zuwa ranar Laraba farashin ya koma Naira 450.

Wata matar aure mai suan A’isha Aliyu, ta koka cewa wahalar man ta sa masu baburan A Daidaita Sahu sun kara kudi, inda yanzu kudin da take kashewa wajen kai ’ya’yanta makaranta ya karu daga Naira 400 zuwa Naira 550.

NNPC ya tabbatar da karin farashin Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya tabbatar da karin farashin litar man fetur a gidajen mansa da ke fadin Najeriya.

Aminiya a zaga gidajen mai a Kano inda ta iske gidan man NNPC da ke titin Club Road na sayar da litar fetur a kan Naira 540.

“NNPC Limited na sanar a abokan hularsa cewa ya kara farashin man fetur da duk gidajen mansa da ke fadin Najeriya, sakamakon sauye-sauyen da aka samu a yanayin kasuwa.

“Duk da cewa muna kokarin samar da kyawawan ayyuka da ganin cewa ba a rasa man ba, amma dole ba za a rasa sauyin farashi ba saboda dalilai na kasuwanci.

“Muna ba da hakuri bisa takurar da wannan sauyin zai haifar,” in ji sanawar da kakain kamfanin NNPC, Garba Deen Muhammad ya fitar a ranar Laraba.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja