Janyewar ruwan Tafkin Chadi ta haifar da nakasu a sana’ar kamun kifi da noman rani

Janyewar ruwan Tafkin Chadi ta haifar da nakasu a sana’ar kamun kifi da noman rani ga al’ummomin kasashen da ke kewaye da tafkin, wadanda yawansu ya kai har sama da miliyan 30.Tafkin Chadi dai ya hade kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Jamhuriyar Afirika ta Tsakiya, inda yake da fadin hekta […]

Janyewar ruwan Tafkin Chadi ta haifar da nakasu a sana’ar kamun kifi da noman rani
Janyewar ruwan Tafkin Chadi ta haifar da nakasu a sana’ar kamun kifi da noman rani

Janyewar ruwan Tafkin Chadi ta haifar da nakasu a sana’ar kamun kifi da noman rani ga al’ummomin kasashen da ke kewaye da tafkin, wadanda yawansu ya kai har sama da miliyan 30.
Tafkin Chadi dai ya hade kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Jamhuriyar Afirika ta Tsakiya, inda yake da fadin hekta dubu 30 da, a shekaru 40 din da suka gabata, a kalla mutane sama da miliyan 30 suna gudanar da sana’o’insu irin su kamun kifi da kiwo da noman rani, a wannan yanki kuma suna more albarkatun sana’o’in nasu, amma yanzu lamarin ya ja da baya. Masana sun yi kiyasin yanzu kasa da mutane miliyan 1 ne ke gudanar da kamun kifi da kiwo da noman ranin, domin abin da ya rage na fadin tafkin bai wuce hekta dubu 2 a maimakon dubu 30 da yake da shi a da ba.
Wannan dalili ya sa wasu masana da kungiyoyi gami da hukumomi ke ta kokarin lalubo hanyoyin farfado da tafkin ta fuskar tarurrukan bita da na kara wa juna sani da zimmar kara wa masunta da manoman yankin kwarin gwiwar gudanar da sana’o’in nasu tare da sa ran matsalar kafewa da janyewar ruwan za ta kau, a koma kamar da.
Babban jami’i a hukumar kula da farfadowar tafkin na Chadi (Lake Chad Basin Sustainable Debelopment Program), Malam Ba’ale Bura ya fada, a jawabin bude taro bita na tsawon kwanaki 3, wanda hukumar ta shirya a garin Maiduguri kwanan baya, cewa ana nan kan wannan kokari na farfado da tafkin.
“ Hukumarmu ta tsara yadda za a rika ziyarar yankunan tare da tattaunawa da mutanen yankin gami kuma da shirya tarurrukan bita don wayar da kawunan mutane sanin muhimmacin wannan sana’a tasu ta kamun kifi da noman rani. Wannan taron bita ne na yadda za a samar da dubarun tsare bacewar kifaye. Mun gayyaci masana da masu sarautun gargajiya domin kowa ya bayar da tasa gudunmuwar kan haka”.  Inji shi.
A kasidar da ya gabatar, Dokta Muhammad Yakubu daga Jami’ar Maiduguri, cewa ya yi farfado da Tafkin Chadin nan ya rataya ne a kan duk wani mai ruwa da tsaki a wannan yanki, musamman ma ga mutanen yankin da kuma masu gudanar da sana’o’i a wannan yankin, kafin a kai ga hukumomi.
Ya ce wajibi ne gwamnatocin wadannan kasashen yankin da ke kewaye da tafkin su zuba hannun jarinsu tare da sa ido don kwato yankin daga rugujewa. “Su kuma masu gudanar da sana’o’i a yankin kada su gaza wajen habaka sana’o’in nasu don cin moriyar yaran da za su taso su gaje su. Ta haka ne kawai za a inganta tattalin arzikin kasashen”. Inji shi.
Wasu mahalatta taron, kamar su Alhaji Kachalla Kyari, Hakimin Wulungo daga yankin karamar Hukumar Dikwa da Alhaji Abubakar Gamandi, Sarkin masunta na Tafkin Chadi da Zanna Malilima Baba Abba Hassan, Hakimi daga Baga, duk bayan nuna farin ciki da godiyarsu ga shirya irin wannan taro, sun kuma koka a dangane da yadda ruwan ya janye, wanda hakan ne ya yi sanadiyyar tsayawar sana’o’in mutanen nasu.
Saboda haka suka yi kira ga gwamnatocin da abin ya shafa, musamman na wadannan kasashe su shigo ciki su taimaka don a farfado da wannan tafki don bunkasuwar tattalin arzikin kasashen yankin. Haka nan sun koka da irin tabarbarewar harkar tsaron yankin, sai suka roki hukumomi su taimaka wajen magance matsalar cikin gaggawa.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno