Japan ta kirkiro akwatin talabijin mai dauke da ‘dandanon abinci’

An zuba wa akwatin talabijin din sinadaran dandano har kala 10.

Japan ta kirkiro akwatin talabijin mai dauke da ‘dandanon abinci’

Samfurin talabijin din da ake iya lasa Hoto: Reuters

Wani Farfesa a kasar, Jappan ya kirkiro wani akwatin talabijin da za a iya lasar fuskarsa da harshe saboda sinadaran dandanon da aka zuba masa don ya ba masu kallonsa damar more kudinsu.

Akwatin talabijin din dai wanda aka sanya wa suna ‘Taste the TV (TTTV)’ an zuba masa sinadaran dandano har kala 10 don ya yi kama da dandanon wani nau’in abinci.

A cewar Farfesan, Homei Miyashita, wanda malami ne a Jami’ar Meiji da ke birnin Tokyo na kasar, sabuwar fasahar za ta bunkasa yadda mutane ke mu’amala da sauran jama’ar da ba sa kusa da su, musamman ma a cikin yanayin annobar COVID-19 da ake ciki.

“Burinmu shi ne mutane su ji kamar suna wajen sayar da abinci daga inda suke, alhalin kuwa suna zaune a gidajensu,” inji shi.

Farfesa Homei dai wanda ya jagoranci ayarin wasu dalibai kimanin 30 a baya dai ya jagoranci kirkiro wasu na’urorin da ke dauke da irin wadannan na’ukan sinadaran, ciki, har da wani cokali mai yatsu da ke kara wa abinci dandano.

Ya dai shafe tsawon shekara daya yana aikin kera wannan akwatin talabijin din, kuma kowane daya ya tashi a kan kusan kudin kasar China Yen 10,000, kwatankwacin kusan Naira 360,000.

Kazalika, tuni Farfesan ya fara tattaunawa da wasu kamfanonin kan yiwuwar fara yin amfani da fasahar tasa kan wasu na’urorin da za a iya saka wa dandanon pizza ko cakulet ko kuma na burodi.

Yuki Hou, wata dalibar Jami’ar ta Meiji mai kimanin shekara 22, ta nuna wa ’yan jarida yadda ake amfani da akwatin talabijin din, inda ta ce masa tana son dandanon cakulet mai zaki.

Bayan ta jarraba maimaitawa, sai wata murya daga cikin talabijin din ta maimaita abin da ta fada, inda ba bata lokaci sai ga abin da ta bukata ya fito daga jikin talabijin din.

“Dandanonsa ya yi kama da na cakuletin madara, akwai zaki sosai kamar cakulet din,” inji ta.