Japan ta yi tashar jirgin kasa don yarinya guda

Hukumar Jiragen kasa ta kasar Japan ta yi shirin rufe wata tashar jirgi da ke wani kauye tsawon shekara uku, amma saboda wata yarinya da ke zuwa makaranta sai aka barta a bude.Jirgin kasa na tsayawa a tasharsa ta Kami-Shirataki a kullum safe da maraice. An yi hakan ne kawai saboda wata yarinya guda ke […]

Japan ta yi tashar jirgin kasa don yarinya guda
Japan ta yi tashar jirgin kasa don yarinya guda

Hukumar Jiragen kasa ta kasar Japan ta yi shirin rufe wata tashar jirgi da ke wani kauye tsawon shekara uku, amma saboda wata yarinya da ke zuwa makaranta sai aka barta a bude.
Jirgin kasa na tsayawa a tasharsa ta Kami-Shirataki a kullum safe da maraice. An yi hakan ne kawai saboda wata yarinya guda ke zaune a Arewacin tsibirin Hokkaido.
Wannan tashar jirgin kasa ta Kami-Shirataki na nuna yadda gwamnata ta damu da kula da al’ummar kasa.
Shekaru uku da suka gabata Hukumar Jirgin kasa ta Japan ta yanke shawarar rufe wannan tasha, saboda babu fasinjoji, kuma inda aka kafata rukukin kauye ne. Tuni dai aka daina hada-hadar sauke kayan ’yan kasuwa. Sai dai hukumomi sun gano wata yarinya ’yar sakandare da ke amfani da jirgin kasa wajen zuwa da dawowa daga makaranta, don haka suka sake shawara. An daidaita kai kawon jirgin  yankin daidai da tafiyar wannan yarinya zuwa makaranta.