Jaridar Daily Trust ta rasa daya daga cikin editocinta

Allah Ya yi wa Editan shafin Ra’ayin Jaridar Daily Trust Malam Ibrahim Auduson rasuwa. Marigayin ya rasu ne yana da shekara 56 a ranar Talatar da ta gabata a Kaduna bayan ya yi fama da ciwon hanta.An haifi marigayin a ranar 21 ga Oktoban 1959 a karamar Hukumar Ibbi ta Jihar Taraba. Kuma an yi […]

Jaridar Daily Trust ta rasa daya daga cikin editocinta
Jaridar Daily Trust ta rasa daya daga cikin editocinta

Allah Ya yi wa Editan shafin Ra’ayin Jaridar Daily Trust Malam Ibrahim Auduson rasuwa. Marigayin ya rasu ne yana da shekara 56 a ranar Talatar da ta gabata a Kaduna bayan ya yi fama da ciwon hanta.
An haifi marigayin a ranar 21 ga Oktoban 1959 a karamar Hukumar Ibbi ta Jihar Taraba. Kuma an yi jana’izarsa a jiya Alhamis da safe kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Marigayin ya yi aiki a matsayin dan rahoto zuwa Babban Wakili zuwa Mukaddashin Editan Labaran Musamman a jaridar Daily Times na tsawon shekaru.
Fitaccen dan jaridar ya kuma yi aiki da Kamfanin Jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo da ke Kaduna daga shekarar 2001 zuwa 2009, kafin ya komo Daily Trust a matsayin Editan Mukala. Ya rasu ya bar mahaifiyarsa da matar aure da ’ya’ya.
Wasu daga cikin abokan aikinsa sun kadu kan rasuwars tasa, inda Dokta Ndagi Umaru wani marubuci a jaridar Daily Trust ya bayyana marigayin da “mutum mai saukin kai da sadaukar da kai ga aiki.”
Shi kuwa Mista Tunde Asaju da ke rubutu a jaridar daga birnin Ontario a kasar Kanada cewa ya yi ya kadu lokacin da ya samu labarin rasuwar fitaccen dan jaridar wanda babban abokin dogaro ne.