Jaridu na amfani da jawabaina wajen bata ni – Jonathan

Shugaban dasa Doka Goodluck Jonathan ya sake caccakar kafafen watsa labarai na dasar nan inda ya zarge su da yin amfani da jawabansa wajen bata shi.Shugaba Jonathan, wanda ke magana a ranar Lahadin da ta gabata lokacin bauta a cocin Apostolic Faith Church da ke Jabi, Abuja, ya ce wadannan ranaku ba su ne ranaku […]

Jaridu na amfani da jawabaina wajen bata ni – Jonathan

Shugaban dasa Doka Goodluck Jonathan ya sake caccakar kafafen watsa labarai na dasar nan inda ya zarge su da yin amfani da jawabansa wajen bata shi.
Shugaba Jonathan, wanda ke magana a ranar Lahadin da ta gabata lokacin bauta a cocin Apostolic Faith Church da ke Jabi, Abuja, ya ce wadannan ranaku ba su ne ranaku mafi dacewa ka yi jawabi ba, saboda kafofin watsa labarai sun fito ne domin yin badin fenti kan duk wata magana da ka yi.
“Ba ni da rubutaccen jawabi saboda mu ’yan siyasa, wadannan ranaku ba su ne ranakun da suka dace ka yi magana ba, domin duk maganar da muka yi, mutane suna neman yadda za su canja ta. Washegari idan ka karanta jaridu sai ka fara shakkun ko abin da ka fada ke nan. Don haka duk wani jawabi da muka a kullum ana bata da ita, amma na ji dadin kasancewa tare da ku a nan. Ina son yara, ina son tsarinku,” inji shi.
Shugaba Jonathan ya ce hade Arewa da Kudu don zama Najeriya wani al’amari ne daga Allah, inda ya ce daukakar Najeriya yana ta’allade ne da bambancenta da albarkatunta da kuma yawan jama’arta.
Ya ce, “Turawan mulkin mallaka sun hade sassan Najeriya ne a 1914. A ranar 1 ga Janairu mai zuwa (shekaranjiya), Najeriya za ta cika shekara 100. Kuma na amince da matsayin limaminmu cewa bah aka kawai hakan ta faru ba, daddara ce ta Ubangiji. Da Ubangiji bai so ba, hakan ba zai faru ba a lokacin, Arewa da Kudu ba za su hade tare ba. Hadewar Arewa da Kudu ta jawo Najeriya ta zama babbar dasa. Na ce Najeriya babbar dasa ce, ba saboda man fetur ba. Domin muna da dasashen da suke hado fetur fiye da Najeriya amma babu wanda ke maganarsu.”
Shugaban ya yi aldawarin ci gaba da sadaukarwar gwamnatinsa na tabbatar da inganta rayuwar masu tasowa, inda ya ce daramin yaron Najeriya ba tare da lura daga inda ya fito ba, yana iya zama Shugaban dasa. “Na yi aldawari ga yaranmu cewa mun sadaukar da kanmu domin tabbatar da sun gaji sabuwar Najeriya. Za mu yi aiki tare domin rusa katangar da ke tsakaninmu, mu kawar da jin cewa ni Kirista ne ko ni Musulmi ne ko Bahaushe ne ko ni Ijaw ne. Da zarar mun rushe wannan katanga za mu fara yadinin cewa dukkanmu ’yan Najeriya ne, kuma mun sadaukar da kai domin ci gaban dasar nan, tabbas ’ya’yanmu za su iske ingantacciyar Najeriya. Za mu dodarinmu, amma ba wannan ne lokacin bayyana abin da muke yi ko abin da ba mu yi, saboda kada su yi tunanin na zo nan ne domin kamfe,” inji shi.