Jaridu sun firgita duniya kan rikicin Najeriya –Baturen Poland, Dokta Mariusz Krasniewski
A makon jiya ne wakilinmu ya hadu da Bature dan kasar Poland mai suna Mariusz Krasniewski (Mariyos Kirinski), a Jami’ar Bayero Kano. Ya kasance manazarci kuma mai bincike game da harshen Hausa. Malami ne shi a Tsangayar Nazarin Al’adun kasashen Yankin Meditireniyan a Jami’ar Polish Academy of Sciences da ke cikin garin Warsaw. A tattaunawa […]

A makon jiya ne wakilinmu ya hadu da Bature dan kasar Poland mai suna Mariusz Krasniewski (Mariyos Kirinski), a Jami’ar Bayero Kano. Ya kasance manazarci kuma mai bincike game da harshen Hausa. Malami ne shi a Tsangayar Nazarin Al’adun kasashen Yankin Meditireniyan a Jami’ar Polish Academy of Sciences da ke cikin garin Warsaw. A tattaunawa ta musamman, ya bayyana wa Aminiya dalilan da suka sanya ya koyi harshen Hausa kuma har yake nazarin al’adun Hausawa. Haka kuma ya bayyana yadda kafafen watsa labarai suka firgita al’ummar duniya kan rikicin Najeriya:
Ga shi kana magana da harshen Hausa sosai, yaya aka yi ka koyi harshen kuma ka iya shi haka?
Na koyi harshen Hausa ne a Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adun Afirka na Jami’ar Warsaw, a kasar Poland. A wannan sashi, ana koyar da harsunan Afirka guda uku, wato Hausa da Swahili da Amharik. Shi yaren Hausa babba ne, domin akwai mutane da yawa da suke magana da shi. A yayin da nake nazarin harsunan uku, na koyi Swahili tsawon shekara daya, Amharic shi ma shekara daya, amma shi harshen Hausa, dayake a kansa ne kadai na yi babban nazari, na fara koyonsa ne tun shekaru goma da suka wuce. Na yi digiri na biyu, sannan na ci gaba na yi digiri na uku. A jami’a, a ka’ida, idan za ka fara nazarin Hausa, shekara hudu za ka yi.
Ka ce ka rubuta littafi da Hausa, ko za ka kara yi mana bayani?
Wannan littafi ne na bincike domin kammala kwas din digiri na uku. Na yi nazari ne game da yadda aka gudanar da cinikin bayi a Najeriya ta Arewa a lokacin mulkin mallaka na Turawa. Wato na yi bincike game da Turawa irin su Mongo Park da sauransu, da suka gudanar da al’amuransu a yankin. Sunan littafin ‘Cinikin Bayi A kasar Hausa.’
Me ya ja hankalinka da ra’ayinka har ka ga cewa ya dace ka koyi harshen Hausa?
Kamar yadda na fada maka a baya, shi harshen Hausa babban harshe ne, wanda a kalla mutane sama da miliyan hamsin ke magana da shi a nahiyar Afirka. A kasashe, musamman kamar Najeriya da Nijar da Sudan da sauransu, akwai mutane da ba su jin Turanci, amma za ka iya mu’amala da su da harshen Hausa, musamman kamar irinmu masu bincike. Abin da ya ja hankalina ke nan ga harshen, kasancewarsa babban harshe a nahiyar Afirka kuma ga shi al’adun Hausawa masu ban sha’awa da burgewa ne. Lokacin da na fara karatu a Jami’ar Warsaw, na rika ganin yadda al’adun Hausawa suke, ta hanyar nazarin da na yi. Al’adun nasu sun burge ni, dalili ke nan ya sanya har na yanke kudurin nazarin harshen har zuwa digiri na uku.
Tun yaushe ne ka fara zuwa Najeriya?
Wannan shi ne karo na biyu da na zo Najeriya. Na zo karo na farko shekaru shida da suka gabata. Na zo nan Jami’ar Bayero Kano ne a lokacin, domin wani taro da ya danganci littattafan Hausa. Akwai wakilai da suka zo daga Jami’ar Warsaw, wanda ina daya daga cikinsu. Sai kuma wannan karon da na dawo nan Jami’ar Bayero makonni biyu da suka gabata.
A wannan karon, me ya kawo ka Najeriya?
Na zo ne domin gudanar da nazari da bincike game da wakokin Hausa na da da kuma na zamani, wato wadanda ake wa lakabi da Hip-Hop. Ke nan zan yi nazari ne game da Adabin Baka da ya shafi gargajiya da kuma na zamani.
Kamar yadda al’adar wasu take na yin zargin bakon al’amari. Ga shi kai Bature ne, amma ka sadaukar da lokaci kana nazarin harshen Hausa, wasu za su yi maka zaton ko kai dan leken asiri ne. Me za ka ce game da haka?
Na farko dai ina son ka gane cewa ni mai bincike ne da kuma nazari, aikina ke nan. Don haka ni ba dan leken asiri ba ne. Al’adun Hausa ne masu ban sha’awa da burgewa, su suka sanya na koyi harshen kuma nake nazari da bincke game da shi, amma ni ba dan leken asiri ba ne. Ba ni da mugun nufi ko kadan ga al’ummar Hausawa da ma sauran al’ummar Najeriya. Amma kamar yadda ka yi mini wannan tambaya, lokacin da na zo nan Kano, wasu mutane suna dari-dari da ni, ganin cewa daga kasashen Turai nake. Na san haka tana faruwa ne saboda yanayin da ake ciki a Najeriya.
Ka koyi harshen Hausa tun kafin ka yi mu’amala da Hausawa, lokacin da ka zo Najeriya, yaya ka iske Hausawa?
Lokacin da na fara zuwa Najeriya na hadu da Hausawa, na dan fuskanci kalubale saboda suna yi mini magana da manyan kalmomin Hausa. Amma na gamu da abokai da yawa, wadanda suka taimaka mini sosai, suka rika ba ni shawara mai amfani. Irin wadannan mutane suna da yawa, wasu ma na mance sunayensu, amma dai muhimmai daga cikinsu sun hada da Farfesa Abdalla Uba Adamu da ke nan Jami’ar Bayero.
A yadda ka hadu da Hausawa yanzu, ya za ka bayyana Bahaushe?
Hausawa suna da kara kuma suna da kirki, wato suna karrama baki. Suna da ban sha’awa, musamman yadda suke son yin ilimi, yadda suke tafiye-tafiye zuwa kasashe daban-daban.
Abincin Hausawa fa, ko kana ci?
kwarai kuwa, ina cin abincin Hausawa. Ina cin danwake kuma lokacin da mutane suka ga ina ci, sai suka rika kallona suna mamaki. Ni kuwa ina jin dadin cin danwake domin yana da kyau da dadi. Haka kuma ina shan fura da nono, ina cin tuwo da miyar kuka.
Me ke burinka na gaba game da harshen Hausa?
Har yanzu ina koyon harshen Hausa ne domin akwai kalmomi da yawa da ban san ma’anoninsu ba, don haka burina shi ne in ga na kware sosai a harshen Hausa. Zan ci gaba da kokari da maida hankali wajen koyon harshen sosai.
Ga shi ka zo Najeriya kuma ka zauna cikin Hausawa, ko akwai wani abu da za ka shaida wa mutanenka na gida, game da haka?
Babban abin da zan gaya musu shi ne abin da ya shafi yadda kafafen watsa labarai ke bayyana musu al’amuran da ke faruwa a Najeriya. A can gida, babu labarin da ake yawan ba su sai na Boko Haram. Labarun da suka shafi tashin hankali, yunwa da talauci da sauransu. Ba a ba da labari mai dadi game da kasar, amma ni yanzu na san ba haka ba ne tunda na zo ga shi ma ina ta mu’alamolina cikin lafiya da annashuwa. Irin wadannan labarai da ake ba kasashen waje, suna sanya tsoro ga zukatan ’yan uwanmu na gida. A lokacin da na zo nan Najeriya, iyayena kan kira ni a waya sosai, suna tambayar ko ina lafiya saboda irin labaran tashin hankali da suke ji ana ba su a kafafen watsa labarai, game da Najeriya. Ni kuwa sai ina gaya musu cewa babu komai, ina lafiya. Ni kaina ina mamakin yadda na ga abubuwan farin ciki da na ci gaba da ke faruwa a Najeriya, amma ba a daukar rahotanninsu zuwa kasashenmu, sai dai na tashin hankali. Ka ga kwanaki a Kaduna, an yi babban taro na makada da mawaka kuma ya burge, ga shi yau kuma a Kano ana taro mai armashi game da Adabin Gargajiya, amma duk babu rahotanninsu a kafafen watsa labarai. Nakan gaya wa mutanena na gida cewa, idan suka zo Najeriya, za su gamu da al’ummar Hausawa, suna da kara da kirki da karimci da mutunci kuma suna da al’ada mai ban shawa’awa. Suna da fina-finai da kade-kade da wake-wake masu dadi. Haka kuma suna da abinci mai dadi.
Batun iyali fa, kana da aure?
Ina da mace daya.
Yadda ka ce kana sha’awar al’adun Bahaushe, idan ka samu mace a nan Bahaushiya, za ka aure ta?
A’a, mu a kasarmu, ba mu auren mata biyu ko uku ko hudu, mace daya muke aure. Amma na ga ’yan matan Hausawa masu kyau da burgewa, sai dai ba mu auren mata da yawa.