Jaridun Kudu da nuna son kai wajen yayata matsalolin al’umma

Muhimmin aikin kafar watsa labarai, rediyo ko jarida ko talabijin shi ne ilimantarwa da wayar da kan al’umma da kuma tabbatar da cewa gwamnatoci a dukkan matakai sun yi abin da ya dace wajen kyautata wa jama’ar da suke mulka. Abu ne da ya dace kafafen watsa labarai su yi aiki ba tare da nuna […]

Jaridun Kudu da nuna son kai wajen yayata matsalolin al’umma
Jaridun Kudu da nuna son kai wajen yayata matsalolin al’umma

Muhimmin aikin kafar watsa labarai, rediyo ko jarida ko talabijin shi ne ilimantarwa da wayar da kan al’umma da kuma tabbatar da cewa gwamnatoci a dukkan matakai sun yi abin da ya dace wajen kyautata wa jama’ar da suke mulka. Abu ne da ya dace kafafen watsa labarai su yi aiki ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ko bangaranci ba, koda matsalar da kafar labarun za ta tabo ko maida hankali a kai, bai shafi al’ummar bangaren da take ba, Kudu ko Arewa.

Al’ummar Jihar Kano da Arewa da ma duk mai zuciyar tausayi sun wayi gari cikin makon jiya da labari mai tada hankali na gano yara 9 ’yan asalin Jihar Kano da wadansu mutane suka sace tare da sauya musu sunaye da kamanni da kuma addininsu na Musulunci zuwa Kiristanci bayan sayar da su a Jihar Anambra. Shekaru da dama iyaye a Jihar Kano ke korafin batar dabo da ’ya’yansu ke yi a lamari mai kama da almara.

Bayan gano yara tara da Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta yi, abin mamaki da takaici, wanda ba shi ne karo na farko ba, shi ne yadda wadansu  kafafen watsa labarai musamman na Kudancin Najeriya suka kawar da kansu daga abin da ya faru, da kuma abubuwa makamantan lamarin na Kano da ke faruwa a Arewacin Najeriya.

A shekarar 2016 kafafen watsa labarai galibi na Kudu sun yi ta yayata labaran wata yarinya mai shekara 15  mai suna Ese Oruru, wadda ta yi soyayya da wani dan asalin Jihar Kano har ta kai ga yarinyar ta biyo shi Jihar Kano daga Jihar Bayelsa inda suka zauna.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan yarinya ba garkuwa saurayin ya yi da ita ba, bisa radin kanta ta biyo shi har Jihar Kano, amma kungiyoyi masu zaman kansu da kafafen watsa labarai na Kudancin Najeriya suka yi ta yayata sabanin ainihin abu da ya faru a tsakaninsu.

Batun gano yaran Jihar Kano a Anambra ya samu halin-ko-in-kula daga shugabanni da kafafen watsa labarai na Kudu, wanda ba shi ne na farko ba an sha yin irin wannan hali a baya.

A duk lokacin da matsala ta kunno kai a Arewa abu ne mai wuya ka ga kafar watsa labarai ta kudancin Najeriya ta yayata domin samar da mafita. Irin wannan abu kan dasa ayar tambaya ko kasar guda ce mai al’umma daya?

Irin bambancin addini da kabilanci da ke zukatan ’yan Najeriya na bayyanuwa a tsarin aiki da kafafen watsa labarai  ke yi wajen tunkarar lamuran da suka shafi kasa wadanda ya kyautu kafar watsa labarai  ta tunkare su yadda ya dace domin neman mafita.

’Yan magana na cewa ‘wanda ya riga ka barci, dole ya riga ka tashi,’ ma’ana Kudancin Najeriya ya sha gaban Arewa wajen samar da kafafen watsa labarai wanda ya sanya kafafen ke ruruta batutuwan da suka shafi al’ummar shiyyar. Magana ta gaskiya lokaci ya yi har ma yana neman wucewa da ’yan kasuwa da ’yan bokon Arewa za su tashi tsaye wajen samar da kafofin watsa labarai da za su rika bayyana wa duniya irin matsalolin da ke ci wa al’ummominsu tuwo a kwarya ciki har da irin wannan batu na satar yara ’yan Jihar Kano.

Dole ne kafafen watsa labarai a fadin Najeriya su rika gudanar da aikinsu ba tare da nuna bangaranci ba, saboda in mutum ba ya zama cikin Najeriya kuma yana karanta wasu daga cikin  jaridun Kudancin kasar nan, zai kaddara kasar a rabe take, sakamakon yadda kafafen watsa labaran ke aiki da son kai.

Domin ciyar da kasa gaba da kuma kasancewarta tsintsiya madaurinki daya, dole kafafen watsa labarai su rika daukar matsala a dukkan sassan kasar nan wajen neman mafita. Sabanin haka wanda shi ke faruwa a halin yanzu babu abin da zai haifar face dasa gaba da kiyayya a tsakanin ’yan Najeriya.

Umar Ahmad Abubakar, dan jarida ne a Gombe. 08080831633