Jarin Bankin Ja’iz ya habaka da Naira biliyan 22

Manajin-Daraktan Bankin Ja’iz Muhammad Nurul Islam ya ce jarin bankin ya habaka da Naira biliyan 22 a cikin shekara 2 da kafa shi.Ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci hedikwatar kamfanin Media Trust masu buga jaridar Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust da kuma Aminiya da ke Abuja  a ranar Litinin da […]

Jarin Bankin Ja’iz ya habaka da Naira biliyan 22
Jarin Bankin Ja’iz ya habaka da Naira biliyan 22

Manajin-Daraktan Bankin Ja’iz Muhammad Nurul Islam ya ce jarin bankin ya habaka da Naira biliyan 22 a cikin shekara 2 da kafa shi.
Ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci hedikwatar kamfanin Media Trust masu buga jaridar Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust da kuma Aminiya da ke Abuja  a ranar Litinin da ta gabata
Ya ce hannun jarin bankin ya shafi dukkan bangarorin tattalin arziki da ke kasar nan, wadanda suka dace da tsarin Musulunci, inda za a yi amfani da dukkan kudin da aka samu a kan abin da ya shafi jama’a.
Ya ce yadda tattalin arzikin bankin ya bunkasa cikin shekaru 2 abin mamaki ne da kuma burgewa, ya ninka yadda na kasar Bangaladesh da kuma sauran bankunan suka samu a Najeriya.
Ya ce banki zai raba kason riba ga wadanda suka zuba jari a bankin.
“Ga shi dai Bankin Ja’iz bai cika shekara 3 a Najeriya ba, amma kudin ajiya a bankin ya kai Naira biliyan 25. Don haka muna da burin bayyana adadin ribar da muka samu, sannan mu ga yadda za mu raba wani kaso ga wadanda suka zuba hannun jari da kuma wadanda suke da asusun ajiya a bankin. Za mu yi hakan ne idan muka samu lasisi a karshen wannan shekarar.” Inji shi.
Ya ce an kai wannan matsayin ne ba wai kawai hadin kan da Musulmin duniya suka bayar  ko kuma hadin kan da mai kudin Afrika ya bayar ba, a’a hadin kai ne daga dukkan jama’ar da suke mu’amala da bankin.
“Muna da adadin Naira biliyan 10 daga wadanda suka zuba hannun jari, sannan masu asusun ajiya sun ajiye Naira biliyan 25, inda kudin da muke da shi a kasa ya kama Naira biliyan 35. Mun zuba hannun jarin Naira biliyan 13 a bangarorin kasuwanci, a yanzu kuma akwai Naira biliyan 22 a hannunmu.” Inji shi.