Jarin bankuna ya karu zuwa Naira tiriliyan 66 —CBN

Duk da kalubalen da ake fuskanta a fannin tattalin arziki, bangaren harkokin banki yana tagazawa.

Jarin bankuna ya karu zuwa Naira tiriliyan 66 —CBN

Bankin CBN

Jarin bankunan Najeriya ya karu daga Naira tiriliyan 10 zuwa Naira tiriliyan 66 a cewa Babban Bankin Kasa.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa bangaren banki yana ci gaba da bunkasa duk matsalar tattalin arziki da ake ciki.

Wani wakili a Kwamitin TsareTsaren Kudi na Bankin CBN, Mista Kingsley Obiora ya bayyana haka, inda ya ce, “Duk da kalubalen da ake fuskanta a fannin tattalin arziki, bangaren harkokin banki yana tagazawa tare da bunkasa cikin nasara.

Jimillar dukiyar bangaren bankuna ta cira sama daga Naira tiriliyan 10.72 a watan Agustan 2021 zuwa Naira tiriliyan 66.76 a Agustan 2022, kamar yadda bayanan Bankin CBN da zuba jari da fadada bayar da rance a muhimman bangarori suka nuna.

“Sakamakon haka, an samu karuwar harkokin tattalin arziki daga Naira tiriliyan 22.62 a Agustan 2021 zuwa Naira tiriliyan 28.12 a wannan lokaci.

“Hakan ya nuna an samu karin kashi 24.3 cikin 100 a muhimman bangarorin tattalin arziki ciki har da man fetur da gas da masana’antu da harkokin gwamnati da na kasuwanci,” in ji shi.