‘Jariraina da na sayar sun hana ni barci’

Wata mace mai suna Esther Simon mai kimanin shekara 26 da ke gudanar da harkokinta a yankin Birnin Tarayya Abuja, ta samu kanta cikin halin tsaka mai wuya, sakamakon sayar da jariranta biyu, daya bayan daya.Matar ta ce ta sayar da jariran ne ga wata malamar jinya mai suna Misis Janet Ofure da ta yi […]

‘Jariraina da na sayar sun hana ni barci’

Biyu daga cikin dakuna uku da malamar jinyar take haya inda kuma ta karbi haihuwar jariran biyu da aka sayar mata a Unguwar Koko a Suleja, Jihar Neja.Wata mace mai suna Esther Simon mai kimanin shekara 26 da ke gudanar da harkokinta a yankin Birnin Tarayya Abuja, ta samu kanta cikin halin tsaka mai wuya, sakamakon sayar da jariranta biyu, daya bayan daya.
Matar ta ce ta sayar da jariran ne ga wata malamar jinya mai suna Misis Janet Ofure da ta yi suna wajen kula da mata masu juna biyu, kuma tana zaune ne a Unguwar Koko cikin garin Suleja ta Jihar Neja.
Misis Esther ta ce jariran nata biyu da ta haife su a wurin malamar jinyar a shekarar 2008 da kuma 2012, na hana ta barci a yanzu, kuma a sakamakon haka, inji ta, ta yanke shawarar amso yaran daga wurin matar da ta sayar wa da su, bayan ta amshi Naira dubu 25 kan kowannensu.
Bayanan da Aminiya ta samu, sun nuna cewa, malamar jinyar ba ta iya cika bukatar Esther Simon na karbo ’ya’yanta ba, wanda a sakamakon haka sai Esther ta garzaya babban ofishin ’yan sanda na “B” Dibision da ke Suleja, inda ta shigar da kara.
Bayanan sun ce a yayin binciken, an kama jami’ar jinyar tare da tsare ta na kwana uku a ofishin, kafin a yanke shawarar mika ta ga Hedkwatar Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja da ke garin Minna domin ci gaba da bincike.
Sai dai kuma wata majiya ta ce ana hanyar kai wadda ake zargi zuwa Minna, babban ofishin yanki na ’yan sanda na Suleja ya bukaci a dawo da ita sakamakon korafin da lauyan wadda ake zargi  ya gabatar a ofishin, bayan ya fahimci cewa za a wuce da ita.  Majiyar ta ce an garzayo da ita wurin, inda aka tsare ta tare da uwar jariran na tsawon kwana uku, inda daga bisani aka ba da belin uwar jariran tare da malamar jinyar, wadanda gaba dayansu ake zargi da gama kai wajen aikata laifi, kuma ’yan sandan sun kai su Kotun Majistare ta Suleja bisa tuhumarsu da laifi.
 Wakilinmu ya ziyarci Kotun Majistare ta Suleja a ranar Litinin da ta gabata inda aka shirya shigar da karar don tuhumar matan biyu, sai dai zaman bai yiwu ba sakamakon janye karar daga wurin. A lokacin da aka tuntubi Babban Kwamandan ’Yan sanda na Suleja Haruna Aliyu, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ofishinsa ya maida al’amarin zuwa sashin binciken manyan laifuffuka (CID) na rundunarsu da ke Minna don ci gaba da bincike.
 Wakilinmu ya je gidan da malamar jinyar ke da zama a Unguwar Koko a Suleja, inda ya samu dakuna biyu a bangarenta a rufe, a yayin da daya ke bude. Wani da ke unguwar da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce wurin nata ya kasance wurin da mata masu ciki ke kai-kawo. Ya ce matan na zuwa wurinta ne don neman kulawa daga gare ta, a yayin da wasu kuma na zuwa ne don ganawa da ita.
Mai Unguwar Koko wanda gidansa ke daura da inda matar take, ba ya gida a lokacin da Aminiya ta nemi jin ta bakinsa, sai dai wakilinsa wanda dansa ne, mai suna Muhammad Auwal Babayaro, ya ce, cikin matan da ke zuwa wurin matar, har da masu aure daga ciki da wajen unguwar.
Ya  ce jami’an duba gari na shashin Hukumar Lafiya a Matakin Farko(PHC) ta karamar Hukumar Suleja na hulda da ita wajen karban haraji,  ya ce baya ga wannan bai san wani abu da ya danganci harkar jarirai ba a game da ita. a lokacin da wakilinmu ya je sashin Hukumar kula da Lafiya a matakin Farko (PHC) na karamar Hukumar Suleja, wata darakta ta bayyana cewa ba ta da masaniya a kan ko an yi wa ungozomar rajista a sahin, sai dai ta ce za su gudanar da bincike a kai don daukan mataki a kan al’amarin.