Jariri dan mako bakwai ya gaishe da mahaifiyarsa da ‘Hello’
Jariri dan makonni bakwai an jiwo yana ce wa mahaifiyarsa ‘Hello,’ wato kalamar gaisuwa ko sannu a cikin harshen Ingilishi. Wadannan jariri an dauki muryarsa a cikin bidiyo. Littattafan da ke bayani kan rainon yara, sun bayyana cewa ka da mutum ya shiga damuwa saboda ’ya’yansa sun kasa magana, ahr sai sun kai watanni 18.Sai […]
Jariri dan makonni bakwai an jiwo yana ce wa mahaifiyarsa ‘Hello,’ wato kalamar gaisuwa ko sannu a cikin harshen Ingilishi. Wadannan jariri an dauki muryarsa a cikin bidiyo.
Littattafan da ke bayani kan rainon yara, sun bayyana cewa ka da mutum ya shiga damuwa saboda ’ya’yansa sun kasa magana, ahr sai sun kai watanni 18.
Sai dai wani abin mamaki, a lokacin da wata uwa, mai suna Belfast, mahaifiyar jariri Toni, ta ga hoton jaririnta dan mako bakwai Cilian ya ce ‘Hello,’ ta cika da matukar mamakin jin wannan gaisuwa.
Da wannan uwa ta tabbatar jaririnta na kwaikwayon maganarta, inda yake kokarin cewa, “Hello,’ sai ta fara aiki akan Kalmar “I lobe you,’ wato ina kaunarka ko ina sonka, ta yadda jaririn zai kwaikwayeta.