Jariri mai hannu da kafa hudu ya bayyana a Indiya

An haifi wani jariri mai hannaye da kafafuwa hudu a garin Baruipur da ke Gabashin kasar Indiya, ind amazauna yankunan karkara ke ikirarin cewa abin bautar Hindu ne ya rikide, aka sake haihuwarsa. An yi wa wannan yaro lakabin sunan yaron ubangiji, sabodaabin bautar Hindu ya sioffantu da yawan kafafuwa. Kuma mutane na ta kwararowa […]

Jariri mai hannu da kafa hudu ya bayyana a Indiya
Jariri mai hannu da kafa hudu ya bayyana a Indiya

An haifi wani jariri mai hannaye da kafafuwa hudu a garin Baruipur da ke Gabashin kasar Indiya, ind amazauna yankunan karkara ke ikirarin cewa abin bautar Hindu ne ya rikide, aka sake haihuwarsa.

An yi wa wannan yaro lakabin sunan yaron ubangiji, sabodaabin bautar Hindu ya sioffantu da yawan kafafuwa. Kuma mutane na ta kwararowa daga ko’ina a yankin,zuwa Jihar Yamamcin Bengal don su yi ido hudu da jaririn.
Su kuwa jami’an ’yan sanda,kokawa suka yi kan yadda suka kasa shawo kan yawan jama’ar da ke ihu da kraji a kan tituna kan lallai sai an kyale su sun shiga asibitin da jaririn ke kwance.
Sai ana ganin wadannan karin hannaye da kafafuwa da ke like a jikin jaririn, alama ce ta dan uwan haihuwarsa da halittarsa ba ta gama cika ba.
Su kuwa iyayen yaron sai dadi suke ji, jin cewa sun samu kari daga alolin Hindu, wato dan abin bauta ubangijinsu na Brahma, wanda aka yi nuni da cewa dama yana da kafafuwa takwas.
“Lokacin da aka ahifi wannan yaro ba mu amincewa wa idanuwanmu abin da muka gnai ba,” a cewar wani daga cikin ’yan uwan jariri, wanda ba a san sunansa ba, a hirar da ya yi da tashar talabijin.
Malaman jinya a asibitin da aka haifi jaririn, sun ce,’ya samu nakasu,’ sai dai wanan wata alama ce daga Ubangiji.