Jariri ya warke daga COVID-19 a Kaduna
An sallami wani jariri dan wata hudu da ya kamu da cutar COVID-19 bayan ya warke a jihar Kaduna. Mutum 149 ke nan suka warke daga cutar a fadin jihar Kaduna zuwa ranar Juma’a 29 ga watan Mayu. Kwamishinar Lafiya Amina Mohammed Baloli ta ce yanzu mutum 76 ne suka rage dauke da cutar a […]
An sallami wani jariri dan wata hudu da ya kamu da cutar COVID-19 bayan ya warke a jihar Kaduna.
Mutum 149 ke nan suka warke daga cutar a fadin jihar Kaduna zuwa ranar Juma’a 29 ga watan Mayu.
Kwamishinar Lafiya Amina Mohammed Baloli ta ce yanzu mutum 76 ne suka rage dauke da cutar a jihar.
COVID-19 ta yi ajalin bakwai daga cikin mutum 232 da suka maku da ita tun farkon bullarta jihar Kaduna.
- Coronavirus: An sallami ragowar masu cutar a Kebbi
- ‘Babu’ sauran mai cutar coronavirus a Taraba
- Asibitoci na kin duba marasa lafiya saboda tsoron coronavirus
Yawan masu cutar na iya karuwa – Baloni.
Amina Baloni ta ce “Yawan masu cutar na iya karuwa saboda karuwar wadanda ke jiran sakamakon gwajinsu.
“An dauki jinin kusan mutum 200. An yi gwaji a wurare 33 a wasu kanana hukumomi 9:
“Chikun, Giwa, Igabi, Kaduna ta Kudu, Kaduna ta Arewa, Makarfi, Sabon-Gari, Soba da kuma Zaria.
Ta ce yawancin masu cutar na da tarihin bulaguro zuwa wasu jihohi ko kusanci da wadanda suka yi tafiya.
Takaita yaduwar cutar.
Don haka, ta ce jami’an lafiya sun dukufa lalubo wadanda suka shigo daga wasu jihohi da wayar da kan jama’a.
“Ma’aikatar Lafiya na bibiyar wadanda suka yi tafiya a cikin yankuna domin dakile yada cutar.
Kaduna ta yi kayan gwajin tafi-da-gidanka
Baloni ta ce yanzu jihar Kaduna ta kara kaimi a gwajin cutar ta yadda za a rika samun sakamako da wuri.
Ta ce motar gwajin cutar da jihar ta sayo ta isa Asibitin Yusuf Dantsoho tana jiran tantancewar hukumar NCDC.
“Ana jiran isowar sauran kayan aiki da na’urorin gwajin da za a kai manyan asibitoci 12 don saukaka gwajin cutar.
Kwamishinar ta ce samun dakunan gwajin tafi da gidanka a kananan hukumomi za su samar da sahihan sakamako.
“Hakan zai taimaka wurin daukar matakan da suka dace wurin yanke hukunci game da sake bude jihar,” inji ta.