Jaririn da aka ce ya mutu ya farfado bayan sa’a 15 a Sin
Wani jariri a kasar Sin da likitoci suka tabbatar da mutuwarsa, bayan an kai shi wuribn adana gawa, ana shirin kone shi, sai kawai ya farfado, kamar yadda gidan talabijin na Zhejia ya ba da labari.Ma’aikatan kone gawa da ke Pan’an a gabashin Lardin Zhejiang, sun shirya kone wannan jariri tyun ranar Juma’a, sai kawai […]
Wani jariri a kasar Sin da likitoci suka tabbatar da mutuwarsa, bayan an kai shi wuribn adana gawa, ana shirin kone shi, sai kawai ya farfado, kamar yadda gidan talabijin na Zhejia ya ba da labari.
Ma’aikatan kone gawa da ke Pan’an a gabashin Lardin Zhejiang, sun shirya kone wannan jariri tyun ranar Juma’a, sai kawai ya ja dogon numfashi, kiamar yadda gidan talabijin din lardin ya bayyana. Wannan yaro dai an tabbatar da mutuwarsa, har ya shafe sa’o’i 15 a wurin adana gawa. Da aka ga yaron ya farfado sai kawai ma’aikatan wurin suka sanar baban jariri, inda aka sake mayar da shi asibiti, a sazshen bayar da kular gaggawa.
“Wannan dais hi ne karon farko da na taba gnain irin wannan ya auku. Tabbas wannan wakni al’amari ne mai ban mamaki,” a cewar likitan asibitin Pan’an, inda aka kwantar da jaririn bakwaini cikin watan Janairu.
Wannan yaro dai ya shafe kwanaki 23 a cikin na’urar dumama jarirai, sannan mahaifinsa ya dauke shi zuwa gida, don su yi bikin sabuwar shekara tare, a ranar Litinin din da ta gabata.
Tushen matsalar wannan jariri dai ta faru tun a ranar 4 ga Fabrairu, bayan an dawo da shi gida. Bayan da likita ya ga zuciyarsa ba ta bugawa, sai kawai ya yanke cewa, ya mutu.
Kafin a kai yaron wurin adana gawa, sai mahaifinsa ya nade shi a cikin bargo rubi biyu, sannan ya sanya shi cikin wata jaka, al’amarin da ake ganin ya ceto rayuwarsa.
Sai dai likitoci sun yi gargadin cewa, da wuya ya warke.