Jaruma Zainab Idris ta amarce

A makon da ya gabata ne fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Zainab Idris ta amarce da angonta wani dan kasuwa a Legas mai suna Mohammed Nafi’u.Bikin wanda aka yi a Kano ya kawo karshen rade-radin da aka dade ana yi cewa jarumar ta yi aure a boye. Haka kuma ya kawo karshen rade-radin da ake yi […]

Jaruma Zainab Idris ta amarce

????????????????????????????????????

A makon da ya gabata ne fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Zainab Idris ta amarce da angonta wani dan kasuwa a Legas mai suna Mohammed Nafi’u.
Bikin wanda aka yi a Kano ya kawo karshen rade-radin da aka dade ana yi cewa jarumar ta yi aure a boye. Haka kuma ya kawo karshen rade-radin da ake yi cewa za ta yi aure da wani abokin sana’arta jarumi Abbas Sani Sadik.
An fara gudanar da shagalin bikin amarya Zainab ne da ‘kamu’, wanda aka gudanar a ranar 7 ga watan Maris, sai kuma hadaddiyar walimar cin abincin dare da aka gudanar a Darul-Tauhid ranar 8 ga watan Maris.
Yayin da aka karkare da daurin aure a Massalacin Ibn Abbas da ke unguwar Shagari kuarters cikin birnin Kano.
An ga fuskokin jarumai mata wadanda suka yi aure a wajen bikin, misali Fati Mohammed da Sakna Gadaz. Haka kuma daga cikin wadanda suka halarci bikin akwai irinsu Hafsat Shehu da Rashida Adamu da Hadizan Saima da Fauziyya Mai Kyau da sauransu.