Jarumai 5 Yarbawa da ke fitowa a fina-finan Hollywood na Amurka
Jaruman biyar dukkaninsu ‘yan asalin kabilar Yarbawa ne daga Najeriya.
Akwai ’yan Najeriya da dama da ake damawa da su a masana’antar shirya fina-finai ta Hollywood da ke kasar Amurka.
Amma a wannan karon za mu yi duba ne akan wasu mutum biyar wanda asalinsu daga kabilar Yarbawa a Najeriya suka fito.
1. Donald Faison
Donald jarumin barkwancin fina-finan Hollywood ne, wanda asalinsa Bayarabe ne. Tauraronsa ya fara haskawa ne yayin da ya fito a matsayin Dokta Chris Turk a shiri mai dogon zango na ‘Scrub’.
2. Gbenga Akinnagbe
Gbenga jarumin fina-finan Amurka ne wanda asalinsa dan kabilar Yarbawa ne daga Najeriya. Jarumin ya yi fice a shiri mai dogon zango na kamfanin HBO.
3. Dayo Okeniyi
Shi ma asalinsa Bayarabe ne, kuma ya fito a fina-finan Amurka da dama. Amma ya fi yin fice a fim din ‘Hunger Games’ da kuma fim din ‘Terminator Genisys’.
4. Olamide Alexander Faison
Olamide, shi ma asalinsa Bayarabe ne daga Najeriya, kuma kani ne ga jarumi Donald Faison. Jarumin ya yi fice a wani shirin gidan talabin na kananan yara mai suna ‘Sesame Stree’’.
5. Rotimi Akinosho
Rotimi asalinsa dan Najeriya ne daga kabilar Yarbawa kuma ya yi fice ne a cikin shiri mai dogon zango na kamfanin Star ‘Boss’ inda ya taka rawa a matsayin Darius Morrison.