Jarumai na shirin fafatawa a bikin karrama zakarun Kannywood
A ranar Asabar da ta gabata ce aka gudanar da wani kwarya-kwaryan biki a Kaduna, inda aka fitar da sunayen jaruman da za su fafata a bikin karrama taurarin fim din Hausa (Kannywood) na bana.Kamar yadda bikin ya gudana, an fitar da sunayen ’yan wasa uku, wadanda a cikinsu ne daya zai iya zama Zakara, […]
A ranar Asabar da ta gabata ce aka gudanar da wani kwarya-kwaryan biki a Kaduna, inda aka fitar da sunayen jaruman da za su fafata a bikin karrama taurarin fim din Hausa (Kannywood) na bana.
Kamar yadda bikin ya gudana, an fitar da sunayen ’yan wasa uku, wadanda a cikinsu ne daya zai iya zama Zakara, a yayin gagarumin bikin da zai gudana a nan gaba. Jaruman sun hada da Sadik Sani Sadik, bisa la’akari da rawar day a taka a fim din Bayan Duhu. Sai kuma Ali Nuhu, wanda ya samu cancantar shiga gasar, bisa la’akari da kokarinsa a fim din Nasibi. Sai kuma na uku, Adam A. Zango, bisa la’akari da kokarinsa a fim din Gwaska.
A bangaren mata kuwa, su ma an fitar da taurari uku, wadanda za su fafata wajen neman daraja ta daya, a yayin bikin karramawar na bana. Jamila Umar, ta cancanci shiga gasar ce, bisa la’akari da kokarinta a fim din Na Hauwa. Sai kuma Nafisa Abdullahi, bisa la’akari da rawar da ta taka a fim din Baiwar Allah. Ita ma Rahama Sadau ta samu shiga rukunin, inda aka yi la’akari da kokarinta a fim din Halalci.
Baya ga wadannan jarumai maza da mata, an kuma zabi wasu na daban, wadanda za su cancanci samun lambobin yabo daban-daban. An ambata sunayen Lawan Ahmad, domin fim din Da’iman da Sadik Ahmad, domin fim din Nasibi da Ali Nuhu, saboda fim din Rumfar Shehu. Sauran sun hada da Ladidi Fagge, saboda fim din Da’iman da Fati Shu’uma, saboda fim din Basma da kuma Fati Washa, bisa la’akari da kokarinta a fim din Hindu.
Abin jira a gani shi ne, a bana ko wane jarumi ne zai zama zakaran-zakaru? A bara dai Sadik Sani Sadik ne ya dauki kambin.