Jaruman bana a bikin ‘2014 Hollywood Golden Globe’
A ranar 12 ga Janairu na badi ne za a gabatar da bikin karrama ’yan fim na duniya a hotel din Beberly Hills da ke birnin Los Angeles da ke Amurka.Bikin, wanda ake wa lakabi da ‘Golden Globe,’ ana gudanar da shi ne a kowace shekara.Wasu daga cikin ’yan fim da aka tace sunayensu domin […]

A ranar 12 ga Janairu na badi ne za a gabatar da bikin karrama ’yan fim na duniya a hotel din Beberly Hills da ke birnin Los Angeles da ke Amurka.
Bikin, wanda ake wa lakabi da ‘Golden Globe,’ ana gudanar da shi ne a kowace shekara.
Wasu daga cikin ’yan fim da aka tace sunayensu domin cancantar karramawa sun hada da Kate Winslet a matsayin ’yar fim da ta zarce kowa a mata. An zabe ta ne saboda kokarin da ta yi a fim din ‘Labor Day.’ Shi kuwa Idris Elba, sunansa ya shiga rukunin dan wasan da ya zama zakara cikin maza, musamman saboda rawar da ya taka a fim din rayuwar Nelson Mandela, ‘Mandela: Long Walk To Freedom.’
Sauran ’yan fim din da sunayensu suka tsallake tantancewa kuma ake sa ran karramawa sun hada da Emma Thompson, saboda fim dinta mai suna ‘Sabing Mr. Banks.’ Akwai kuma Dame Judi Dench.
A bikin na badi, fina-finan da aka tantace domin fafatawa a gasar fim mafi burgewa ta fuskar wasan kwaikwayo a 2014 sun hada da: ‘12 Years A Slabe’ da ‘Captain Phillips’ da ‘Grabity’ da ‘Philomena’ da ‘Rush.’
A bangaren fina-finan waka ko na barkwanci kuwa, an tantace: ‘American Hustle’ da ‘Her’ da ‘Inside Llewyn Dabis’ da ‘Nebraska’ da ‘The Wolf of Wall Street.’
A bangaren ’yan wasa masu mara wa jarumi baya kuwa, an tantance sunayen Barkhad Abdi, a fim din ‘Captain Phillips’ da Daniel Bruhl, a fim din ‘Rush’ da Bradley Cooper, a fim din ‘American Hustle’ da Michael Fassbender, a fim din ‘12 Years A Slabe’ da kuma Jared Leto, a fim din ‘Dallas Buyers Club.’
Ta bangaren masu mara wa jarumai mata baya kuwa, an tantance sunayen ’yan fim kamar: Sally Hawkins, a fim din ‘Blue Jasmine’ da Jennifer Lawrence, a fim din ‘American Hustle’ da Lupita Nyong’o, ta fim din ‘12 Years A Slabe’ da Julia Roberts, ta fim ‘August: Osage County’ da June Skuibb, ta fim din ‘Nebraska.’
Sauran bangarorin da za a karrama sun hada da darakta mafi kwarewa da shirin wasan kwaikwayo a talabijin mafi inganci da sauransu.