Jaruman Bollywood 10 da aka haifa a watan Disamba
Jaruman sun yi fice a masana’antar fim ta Bollywood.
Ganin yadda muke shirin bankwana da 2021, hakan ya sa Aminiya ta yi duba tare binciko wasu jarumai maza da mata daga Bollywood da aka haifa a watan Disamba.
Wadannan jarumai sun yi fice tare da taka muhimmiyar rawa a masana’antar fim ta Bollywood.
- An cafke masu garkuwa da mutane 11 a Taraba
- Najeriya A Yau: Dalilan ‘rashin yanke wa masu laifi’ hukunci a Najeriya
1. Dia Mirza
Jaruma ce da ta yi fice a Bollywood kuma tana daya daga cikin mata masu kyau a masana’antar. An haife ta a ranar 9 ga watan Disamba 1981.
2. Salman Khan
Fitacce, shararren jarumi, mawaki kuma mai shiryawa. Salman Khan ya jima ana damawa da shi a Bollywood, ya ga jiya ya kuma ga yau. An haife shi a ranar 27 ga watan Disamba 1965.
3. Sohail Khan
Sohail kani ne ga jarumi Salman Khan. Shi ma kamar dan uwansa jarumi ne kuma mai shirya fina-finai. An haife shi a ranar 20 ga watan Disamba 1970.
4. Ankita Lokhande
Lokhande ma’aikaciya ce a Bollywood wadda daga baya ta fara fitowa a fina-finai, ta fito a fim din ‘Baaghi 3’ da ‘Manikarnika’. An haife ta a ranar 19 ga watan Disamba 1984.
5. Payal Rajput
Jaruma ce da ta fi fitowa a fina-finan Telugu da Punjabi, an haife ta ranar 5 ga watan Disamba 1992.
6. John Abraham
Jonh mai shirya fina-finai ne kuma fitaccen jarumi a Bollywood, ya fito a fina-finai masu tarin yawa. An haifi John Abraham a ranar 17 ga watan Disamba 1972.
7. Anil Kapoor
Anil Kapoor fitaccen jarumi ne da ya yi kaurin suna wajen fitowa a fina-finan Bollywood, kazalika jarumin ya fito a shiri mai dogon zango na Hollywood ’24’.
An haife shi a ranar 24 ga watan Disamba 1956.
8. Dheeraj Dhoopar
Dhoopar jarumi ne da ya yi fice da shura a Bollywood, musamman a shirin gidan talabijin mai dogon zango na ‘Kundali Bhagya (This is Fate)’. An haife shi a ranar 20 ga watan Disamba 1984.
9. Richa Chadda
Richa jarumai ce a Bollywood kuma ta fito a fina-finai da dama, ita ma an haife ta a ranar 18 ga watan Disamba 1986.
10. Boman Irani
Fitaccen jarumi, mai barkwanci, mai daukar hoto, dan wasan dandamali kuma mai shirya fina-finai. Boman ya yi shura matuka a Bollywood, an haife shi a ranar 2 ga watan Disamba 1959.