Jaruman Kannywood 5 da suka taba yin takarar siyasa
Jaruman su ma sun fito an dama da su a siyasance.
Akwai wasu fitattun jaruman masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood da suka taba tsayawa takarar siyasa a matakai daban-daban a yankunansu.
A bisa dokar kasa dai, kowane dan kasa na da ’yancin tsayawa takarar wata kujerar shugabanci, matukar ya cika sharuda da ka’idojin da Hukumar Zabe ta INEC da Kundin Tsarin Mulki suka tanadar.
Ga sunayen jaruman da kuma mukaman da suka taba tsayawa takara a kai:
1. Hamisu Iyantama
Fitaccen jarumin Kannywood ne da aka dade ana damawa da shi a masana’antar kuma ya taba tsayawa takarar kujerar Gwamnan Jihar Kano a karkashin tutar jam’iyyar ND a 2007.
Sai dai a lokacin, Malam Ibrahim Shekarau na jam’iyyar ANPP ne ya lashe zaben Gwamnan.
2. Alasan Kwalle
Shi ma tauraro ne kuma daya daga cikin masu ruwa da tsaki a Kannywood.
Jarumin, ya taba tsayawa takarar kujerar Shugaban Karamar Hukumar Ungogo a 2007 a jam’iyyar PDP, wanda a lokacin ya kare a matsayin dan takarar Mataimakin Shugaban Karamar.
Alasan Kwalle ya sake tsayawa takarar kujerar Kansila a mazabar Bachirawa da ke Karamar Hukumar ta Ungogo, amma a karkashin jam’iyyar APC a shekarar 2015.
A yayin zantawarsa da Aminiya, Kwalle ya bayyana cewar yana da sha’awar sake fitowa takarar dan Majalisar Jihar Kano a nan gaba.
“Ina nan zan fito takarar dan Majalisar Jiha a Kano, amma a yanzu ban san jam’iyyar da zan fito a ciki [ba], APC ko PDP ban sani ba sai nan gaba kadan,” a cewar Kwalle.
3. Nura Hussain
Daya ne daga cikin jarumai maza a Kannywood da suka fi dadewa kuma sananne ne a masana’antar.
A shekarar 2007, ya fito takarar Kansila a mazabar Yakasai da ke Karamar Hukumar Birni da Kewaye a Jihar Kano.
4. Abba El-Mustapha
Wanda aka fi sani da ‘Abba Ruda’ shi ma ya jima ana dama wa da shi a Kannywood.
Kuma ya taba fitowa neman takarar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano, karkashin jam’iyyar PDP a 2015.
Sai dai bai kai labari ba, domin bai yi nasarar samun tikitin tsayawa takarar ba.
5. Lawan Ahmad
Ya dade tauraronsa yana haskawa a Kannywood.
Jarumin ya nemi tsayawa takarar dan Majalisar Dokokin Jihar Katsina a 2019, karkashin jam’iyyar APC, amma bai samu nasarar samun tikitin takarar ba.