Jarumar Kannywood Fati Slow ta rasu
Allah Ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Slow Motion, rasuwa a kasar waje
Allah Ya yi wa tsohuwar jarumar masana’antar Kannywood, Fati Slow Motion, rasuwa a kasar waje.
A safiyar Talata tsohuwar tauraruwa e Kannywood, Mansura Isa ta sanar da rasuwar ta shafinta na Facebook.
Mansura, wadda ta yi addu’ar samun rahama da Fati Slow ta ce marigayiyar ta rasu ne da daddare a kasar waje, kuma a can za a yi jana’izarta.
Ta ce, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
- Buratai ya bukaci sojoji su gaggauta murkushe ’yan ta’addanci
- Don maslahar Kano aka dawo da Sarki Sanusi II — Gwamnati
“Allah Ya yi wa Fati Slow rasuwa jiya da daddare a Abeche kusa da Sudan.
“A can za a yi jana’izarta, amma ana zaman makoki a gidansu da ke Unguwar Uku.”
Fati Slow Motion tana daga cikin jaruman Kannywood da suka yi tashe a shekarun 2000.
A baya-bayan nan Fati Slow Motion ta yi tashe a kafofin sada zumunta, saboda amfani da kalmomi ‘Kebura’ da kuma ‘No body is Fafet’.
Wani shugaban al’ummar Hausawa a birnin Abeche, hedikwatar Lardin Ouaddai da ke Gabashin kasar Chadi ya tabbatar wa Aminiya da rasuwar Fati Slow, a safiyar Talata.
Bisa alamu, Fati Slow ta ɗan zauna a Abeche na dan wani lokaci, kafin ita da mijinta su koma garin Tina a kan iyakar kasar Chadi da Sudan, inda Allah Ya yi mata rasuwa.