Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure

Jarumar ta shammaci mutane tare da yin aure a lokacin da ba zato ba tsammani.

Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure

Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta yi aure da masoyinta, Ibrahim Garba.

An ɗaura auren a ranar Asabar a Masallacin da ke Unguwan Rimi, a Jihar Kaduna, bayan Ibrahim ya biya sadaki Naira 300,000.

Rahama, ta sanar da ɗaurin auren a shafinta na Facebook, inda ta gode wa Allah tare da neman addu’a daga masoyanta.

Ta bayyana farin ciki da godiyarta, tare da fatan wannan sabon babi na rayuwarta zai kasance mai albarka.

Auren mata na zuwa ne watanni biyu bayan rasuwar mahaifinta, Ibrahim Sadau.

’Yan uwanta sun yaɗa hotuna da bidiyon bikin a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka yi mamakin yadda aka yi bikin ba tare da sanin jama’a ba.

Rahama, wacce furodusa ce a Kannywood, an naɗa ta memba a Kwamitin Fasaha na shirin Investment in Digital and Creative Enterprise (iDICE).

An ba ta muƙamin ne a 2024 ƙarƙashin ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.