Jarumar Nollywood Tonto Dikeh ta bayyana sha’awar Musulunci

Jarumar ta ce kiran sallah yana matuƙar kwantar mata da hankali.

Jarumar Nollywood Tonto Dikeh ta bayyana sha’awar Musulunci

Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Tonto Dikeh, ta fito fili ta nuna jin daɗinta ga addinin Musulunci.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar Talata, ta bayyana yadda ta yi zamanta a kusa da wani masallaci tsawon shekara huɗu tana jin kiran sallah a kullum.

“Idan tashi da safe mafi kyawun sauti a kowace rana da nake ji shekaru huɗu da suka gabata… sauti na ƙauna da sadaukarwa, sautin kyawun ga son Allah da ƙauna.”

Dikeh, ta kuma nemi hanyoyin tallafa wa masallacin fiye da taimakon kuɗi, inda ta nemi mabiyanta su ba ta shawarwari.

“Idan na so na yi sadaka ga Masallaci, me zan iya bayarwa baya ga kuɗi?” kamar yadda ta wallafa.

Jarumar ta yaba da sadaukarwa da kuma niyyar  Musulmai, inda ta bayyana cewa, “Allah shi ne abin so. An taɓa ni sosai. Babbar addu’ata ita ce fahimtar addinin Musulmi. Sadaukarwarsu da niyyarsu ta cancanci a kwaikwaya.”

Dikeh jaruma ce a masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood, sannan kuma  ‘yar siyasa.

A babban zaɓen 2023, ta fice daga jam’iyyar ADC zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Ita ce mataimakiyar gwamnan Jihar Ribas a jam’iyyar ADC a zaɓen 2023.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara