Jarumi Mirza zai yi aure
Fitaccen jarumi kuma furodusan fina-finan Indiya Dia Mirza zai auri masoyiyarsa Sahil Sangha a ranar 18 ga Oktoba, 2014 a birnin Delhi da ke kasar IndiyaYa ce: “Shirye-shiryen bikinmu sun kankama har mun sanya ranar 18 ga Oktoba, 2014 a matsayin ranar aurenmu. Wannan ce ranar da za a daura mini aure da Sahil.”Bikin wanda […]
Fitaccen jarumi kuma furodusan fina-finan Indiya Dia Mirza zai auri masoyiyarsa Sahil Sangha a ranar 18 ga Oktoba, 2014 a birnin Delhi da ke kasar Indiya
Ya ce: “Shirye-shiryen bikinmu sun kankama har mun sanya ranar 18 ga Oktoba, 2014 a matsayin ranar aurenmu. Wannan ce ranar da za a daura mini aure da Sahil.”
Bikin wanda za a gudanar da shagalinsa a birnin Delhi za a gayyaci abokai da kuma na kusa da iyalin ma’auratan.
Za a gudanar da kasaitacciyar dina a Mumbai, inda jarumin ya gayyaci manyan abokansa daga bangaren masana’antar fina-finan Indiya.