Jarumin Bollywood Dilip Kumar ya rasu

Ya fara fitowa a cikin wani fim mai suna Jwaar Bhaata.

Jarumin Bollywood Dilip Kumar ya rasu

Shahruk Khan tare da marigayi Dilip Kumar

Dilip Kumar, daya daga cikin fitattun taurarin fina-finan Indiya, ya riga mu gidan gaskiya yana shekara 98.

Tauraron jarumin ya haska a fina-finai fiye da 65 a tsawon shekaru 50 da ya shafe yana taka rawar gani a matakai daban-daban.

A ranar 30 ga watan Yuni ne aka kwantar da shi a Asibiti a lokacin da ya fara fama da matsalar numfashi, wanda tun kafin nan ya rika fama da jinya ta tsawon watanni.

Ya rasu ya batar matarsa daya jal, Saira Banu, daya daga taurarin masana’antar Bollywood.

Jarumai, ’yan siyasa da kuma masana tarihi, na ci gaba da kwarara alhini kan wannan rashi cikin sakonni daban-daban a shafukan sada zumunta.

Jaridar Indian Times ta wallafa wani hoto na jarumin nan Shahruk Khan, yana rarrashin Saira yayin da ya je ta’aziyya.

Haka kuma, wani hoto da jaridar ta wallafa ya nuna jarumi Ranbir Kapoor yana isa gidan marigayin wanda jami’an ’yan sanda suka yi wa kawanya.

A watan Dasumba na shekarar 1922 aka haifi Dilip Kumar a Peshawar wanda a yanzu garin ya koma yankin kasar Pakistan gabanin a rarraba kasar Indiya.

Kasancewarsa musulmi, ainihin sunan da aka rada masa shi ne Muhammad Yusuf Khan, amma ya shiga masana’antar Bollywood da suna Dilip Kumar na al’adar mutanen Indiya kamar yadda sauran abokan aikinsa suke yi.

Ya fara fitowa ne a cikin wani fim mai suna Jwaar Bhaata a shekarar 1944, amma fim din Andaz ya fito a shekarar 1949 ya sanya tauraruwarsa ta haska a duniya.

Fim din Andaz wanda aka yi shi kan soyayya, akwai jarumai irinsu Nargis da Raj Kapoor da suka fito a cikinsa.