Jarumin Bollywood Sanjay Dutt ya kamu da cutar sankara

Nan ba da dadewa ba zan shawo kan cutar sannan zan fara aiki a kan sabon fim dina a watan Nuwamba.

Jarumin Bollywood Sanjay Dutt ya kamu da cutar sankara

Sanjay Dutt

Daya daga cikin fitattun Jaruman dandalin Bollywood na fina-finan Indiya, Sanjay Dutt, ya kamu da cutar sankara wato kansa, wadda wasu ke kira cutar daji.

Jarumin mai shekaru 61 a duniya wanda ya fito a fina-finai fiye da 150, ya tabbatar da hakan a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Tabbacin kamuwa da cutar kansa da Sanjay Dutt ya bayar ya biyo bayan makonni da aka shafa ana yada jita-jitar hakan a kafafen sadarwa na kasar Indiya.

A wani rahoto da jaridar BBC ta wallafa ya ruwaito jarumin yana cewa, “nan ba da dadewa ba zan shawo kan cutar sannan zan fara aiki a kan sabon fim dina a watan Nuwamba.”

A watan Agustan da ya gabata ne jarumin ya kamu da cutar Coronavirus bayan ya fuskanci matsalar shaker numfashi.

Sakamakon gwajin da aka yi masa a asibitin Mumbai Lilavati, ya gano yana dauke da cutar Coronavirus da wasu cututtukan na daban.