Jarumin fim din ‘Black Panther’ Chadwick Boseman ya rasu

Jarumin fim dan kasar Amurka Chadwick Boseman, wanda ya yi fice a fim din Black Panther, ya rasu. Sanarwar rasuwar Chadwick, ta jefa masoya da masu harka a masana’atar fim a fadin duniya cikin alhini. Mai shekara 43 din ya rasu ne a Los Angeles sakamakon cutar kansa da ya shekara hudu yana fama da […]

Jarumin fim din ‘Black Panther’ Chadwick Boseman ya rasu

Jarumin fim dan kasar Amurka Chadwick Boseman, wanda ya yi fice a fim din Black Panther, ya rasu.

Sanarwar rasuwar Chadwick, ta jefa masoya da masu harka a masana’atar fim a fadin duniya cikin alhini.

Mai shekara 43 din ya rasu ne a Los Angeles sakamakon cutar kansa da ya shekara hudu yana fama da ita.

Amma bai taba tattauan batun rashin rafiyar tasa a bainar jama’a ba, yayin da ya ci gaba yi aikin manyan finafinan Hollywood a yayin da sau dama aka masa tiyata, kamar yadda iyalansa suka bayyana.

Sakon rasuwar da suka fitar ya ce “Chadwick, Mayakin gaske ya jure cutar har ya kawo muku fina-finai da dama da ke matukar kauna”.

Iyalan sun ce fina-finansa na Marshall, Da 5 Bloods, August Wilson’s Ma Rainey’s Black Bottom da sauransu duk an yi su ne a tsakanin lokutan da aka yi masa tiyata.

“Babbar karamcin da ya samu a tarihin rayuwarsa na jarumi shi ne matsayin da ya samu na farkar da Sarki T’Challa a fim din Black Panter, inji sanarwar.

Shaharar Boseman

A 2013 Boseman ya fara yin fice ne a 2013 bayan ya fito a fim tare da fitaccen dan wasan kwallon baseball, Jackie Robinson a fim din 42.

Sai kuma a 2014 da ya fito a fim din Get on Up tare da mawaki James Brown.

Amma za a fi tuna shi da fim din Black Panther, daya ga cikin manyan finafinan 2018.

A cikin fim din Boseman ya fito a matsayin sarkin Wakanda, wani garin ‘yan Afirka wanda ya fi ko’ina ci gaban fasa a duniya.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno