Jarumin fim din ‘Hangober’ Justin Bartha ya yi aure a Hawaii
A ranar Asabar ta makon jiya Justin Bartha, jarumin shahararren fim din ‘Hangober’ ya auri ’yar fim Lia Smith.dan fim din, wanda a bana ya cika shekara 35 a duniya, ya auri budurwar tasa ce a tsibirin Oahu da ke Kualoa Ranch na birnin Hawaii. Wani abin tarihi kuma shi ne, a wannan tsibiri ne […]

A ranar Asabar ta makon jiya Justin Bartha, jarumin shahararren fim din ‘Hangober’ ya auri ’yar fim Lia Smith.
dan fim din, wanda a bana ya cika shekara 35 a duniya, ya auri budurwar tasa ce a tsibirin Oahu da ke Kualoa Ranch na birnin Hawaii. Wani abin tarihi kuma shi ne, a wannan tsibiri ne aka dauki shirin fim din ‘The Hunger Games’ kamar yadda mujallar ‘E’ ta ruwaito. Tun farko dai, ma’auratan sun yi baiko ne a bara.
A yayin daurin auren, baya ga ango da amarya, akwai kuma mai koya musu atisaye. Akwai kuma wasu daga cikin ’yan uwa da abokan arziki, wadanda suka hada da Reese Witherspoon da mijinta Jim Toth. Sauran sun hada da jarumin fim din ‘Social Network,’ Jesse Eisenberg da kuma Ken Jeong, wanda tare da Justin suka fito cikin fim din ‘Hangober.’
Lia Smith dai ba ita ce budurwa ta farko da Justin ya taba nema ba, domin kuwa ya taba yin soyayya da Ahsley Olsen har ta tsawon shekara biyu, inda suka rabu a cikin watan Mari
s na 2011.