Jarumin fim din Hausa Malam Waragis ya rasu

  Allah Ya yi wa jarumin fim din Hausa Malam Muhammad Umar Jos wanda aka fi sani da Malam Waragis ya rasu a garin Jos da ke Jihar Filato.   Al’amin Ciroma ya wallafa a shafinsa na facebook cewa jarumin ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya na tsawon lokaci.   Tuni aka […]

Jarumin fim din Hausa Malam Waragis ya rasu

 

Allah Ya yi wa jarumin fim din Hausa Malam Muhammad Umar Jos wanda aka fi sani da Malam Waragis ya rasu a garin Jos da ke Jihar Filato.

 

Al’amin Ciroma ya wallafa a shafinsa na facebook cewa jarumin ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya na tsawon lokaci.

 

Tuni aka yi jana’izar mamacin a garin Jos kamar yadda shara’ar musulunci ta tanadar.