Jarumin Kannywood Sani SK yana neman taimako

Jarumin ya wallafa faifan bidiyo, inda ya bukaci al’umma su taimaka masa.

Jarumin Kannywood Sani SK yana neman taimako

Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood wanda aka dade ana damawa da shi, Sani SK, yana fama da rashin lafiya, har ya kai ga ya fito yana neman taimakon kudi domin a duba lafiyarsa.

A wani bidiyo da Aminiya ta gani, Sani SK ya ce yana matukar bukatar taimakon ne domin kula da lafiyarsa.

Jarumin ya tabbatar da cewa an taimaka masa, sai dai yana bukatar karin taimako, hakan ne kuma ya sa ya yi bidiyo domin a ga halin da yake ciki.

  1. Yadda barayi suka addabi majinyata a asibitin Gombe
  2. ’Yan bindiga sun kashe mutum 40 a kauyukan Zamfara

A bidiyon, daga kallo daya za ka gane jarumin yana fama da rashin lafiya.

Jim kadan bayan bidiyon ya fito, wasu mutane suka fara caccakar ’yan Kannywood cewa ba sa taimakon junansu.

Martanin Fauziyya D. Sulaiman

Da take tsokaci a kan halin da Sani SK yake ciki, Fauziyya D. Suleiman, fitacciyar marubuciya wadda kuma ta yi fice wajen taimakon jama’a a ciki da wajen Kannywood, ta ce jarumin yana bukatar taimako, ta kuma yi kira a taimaka don Allah ba tare da cin mutuncin ’yan Kannywood ba.

A cewarta, “Tun da Sani SK ya saki bidiyon nan mutane ke ta tambayar lambar waya da asusun bankinsa, don haka na kira shi ya turo da kansa.

“Amma abin da na ke so mutane su gane,  SK ya jima yana jinya; na san wani daga irin taimakon da abokan sana’arsa suka ba shi.

“Kai, hatta ta sanadiyyata mutane da yawa sun taimaka masa, mu ma mun sha saya masa magani, sannan mun biya wa yaransa su biyu kudin makaranta.

“Don haka ita jinya duk taimakon da za a yi maka ba za a iya mata ba, musamman shi da ya kwashe shekaru yana jinya, a tare da ni ’yan fim sun sha yi masa gidauniya.

“Don haka wanda zai taimaka ba sai ya zagi kowa ba, ya yi domin Allah da kuma kasancewarsa dan uwa Musulmi, domin ita jinya ba ta wuce kan kowa ba.”

Sannan a karshe ta ba da asusun ajiyar bankin jarumin, da lambar wayarsa.

Asusu: 0069811811

Banki: Sterling Bank

Lambar waya: 08037030617