Jarumin maza
Wani mutum ne za shi masallaci da asuba, yana sanye da babbar riga. Yana cikin tafiya sai ya ji ana neman taimako, ana cewa: “A tare! A tare!!” Sai ya sa babbar rigarsa ya rufe dabbar da ita ya cacume ta. Shi a zaton sa akuya ce aka koro. Mutanen da suka biyo ta sai […]
Wani mutum ne za shi masallaci da asuba, yana sanye da babbar riga. Yana cikin tafiya sai ya ji ana neman taimako, ana cewa: “A tare! A tare!!” Sai ya sa babbar rigarsa ya rufe dabbar da ita ya cacume ta. Shi a zaton sa akuya ce aka koro. Mutanen da suka biyo ta sai suka ce masa: “Baba, lallai kai jarumi ne mara tsoro.” Shi kuwa ya ce: “kwarai kuwa, ai na gaji jaruntaka daga babana!” daya daga cikin mutanen sai ya ce wa daya: “Miko mini takunkumin nan in sanya mata.” Da mutumin ya ji haka sai ya ce: “Yaro, me na kama ne?” Ya ce masa: “Kura ce!” Nan take ya tsure da zawo!
Daga Salisu A. Jaji, 07031063622