Jarumin Nollywood Papa Ajasco ya rasu
Mista Ogunrombi ya shahara saboda rawar da ya taka a cikin fim din Papa Ajasco.
Fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina–finai ta Kudancin Najeriya ta Nollywood, Femi Ogunrombi wanda aka fi sani da Papa Ajasco, ya rasu.
Wani mai ruwa da tsaki a harkokin wasan kwaikwayo, Husseini Shaibu ne ya tabbatar da rasuwarsa cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi.
- Arsenal ta cije kan Mudyryk, ana shirin cefanar da United, Depay zai ci gaba da zama a Barcelona
- 199 daga cikin likitoci 280 da muke biyan albashi na bogi ne —Matawalle
Ya rubuta cewa, “A yanzu na samu labarin cewa masanin kida, tsohon mai koyar da waka a NATIONALTROUPE kuma wanda ya fito a matsayin ‘Papa Ajasco’ a cikin shahararren shirin barkwanci na #waleadenugaprod ‘Papa Ajasco’, Mista Femi Ogunrombi ya rasu.
“An sanar da ni cewa dan wasan kwaikwayon, mawaki, babban jarumi kuma kwararren ma’aikacin jinya wanda muke kira ‘Uncle Ogurombo’ ya rasu a Yammacin yau (Asabar).”
Mista Ogunrombi ya shahara saboda rawar da ya taka a cikin fim din nan na barkwanci mai dogon zango wanda Wale Adenuga ya shirya mai suna Papa Ajasco.
Ogunrombi ya fito a matsayin Papa Ajasco a cikin shirin mai wannan suna bayan ya maye gurbin Abiodun Ayoyinka da aka soma fim din da shi.