Jawabin Shugaba Buhari
Bayan jawabin dawowa daga jiyya da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, masu fashin baki suka fara sharhi da tsokaci. Wasu na gwalashewa, suna ganin jawabin ba ya dauke da wani muhimmin abu da ba a taba ji ba,wasu kuwa na ganin wannan shi ne jawabi mafi tsaruwa da shugaban ya taba yi. Ni kuwa nawa […]
Bayan jawabin dawowa daga jiyya da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, masu fashin baki suka fara sharhi da tsokaci. Wasu na gwalashewa, suna ganin jawabin ba ya dauke da wani muhimmin abu da ba a taba ji ba,wasu kuwa na ganin wannan shi ne jawabi mafi tsaruwa da shugaban ya taba yi. Ni kuwa nawa ra’ayin, jawabin ya yi, ba wai don tsawonsa ko gajartarsa ba. A’a jawabin ya kunshi wasu batutuwa da yanzu ake ta kokarin tadowa, kuma kowa da tasa manufar.
Na farko, batun masu kokarin a sauya fasalin kasar. Shugaba Buhari ya riga ya fitar da matsaya guda cewa, duk mai korafi game da sake fasalin Najeriya, to ya doshi ko majalisar dokokin kasar ko ta zartarwa, domin su ne halatattun hukumomin da za su iya duba yiwuwar sake taswira da zamantakewar Najeriya. Kamar yadda muka sani, akwai wasu yankuna na kasar nan, da kungiyoyin ta kife da ba za su yi na’am da wannan jawabi na Buhari ba, saboda wadannan yankuna da kungiyoyi irin kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, da kungiyar masu hankoran kafa kasar Biyafara, wato IPOB, duk ba za su so jawabin shugaban kasa ba. Kazalika, ‘yan-bokon kudancin kasar nan, wadanda sun dade suna yekuwar sake sauya fasalin Najeriya, su ma ba za su ji dadin wannan jawabi ba.
Abin da Shugaba Muhammadu Buhari ya fadi, shi ne abin da kundin tsarin mulkin kasar ya amince, wato “kasancewar Najeriya dunkulalliyar kasa” ba muhawara kansa. Amma su kungiyoyin ta kife kamar Afenifere NEDECO da IPOB,da ‘yan bokon yankin Kudu, irin su Farfesa Wole Soyinka da mutanensa, duk sukan yi fatali da abin bai musu dadi ba, ko da kuwa yana cikin kundin tsarin mulki.
Duk masu kishin kasa kamata ya yi a yi maraba da jawabin Shugaba Muhammadu Buhari, domin su masu rajin wannan ra’ayi sai an canza fasalin Najeriya, suna so ne kawai su je fa Najeriya cikin rudani, domin su musamman wadanda suka fito daga kudancin kasar nan, suna so, wai ko dai ai amfani da rahotan taron da tsohon shugaban kasa GoodLuck Jonathan ya shirya gab da zaben 2015 ko kuma a kira shugabannin kabilun kasar kamar irin su, Afenifere da IPOB da Ohanzae da ACF da OPC da sauransu, wai wadannan shugabannin kabilun su ne, za su tattauna yadda Najeriya za ta kasance.
Shugaba Muhammadu Buhari ya fahimci cewa,ba ta yiwu a dora Najeriya bisa tubalin kabilanci kamar yadda mutanen can ke so . Domin a hukamance ma kawai, Najeriya na kunshe da sama da kabilu 250, amma wasu masana na cewa kabilun sun fi 400. Akwai masana da suka ce, ko Jihar Adamawa kawai na da kabilu kusan 20, inda Jihar Taraba je da sama da 50. A kudancin Kaduna na da kabilu daban-daban, kuma kabilun Najeriya sun warwatsu ko’ina a fadin kasar nan, sannan wasu su ce so suke a dora kasar bisa tsarin kabilanci? Wannan babban kuskure ne. Yadda kabilanci yai sanadiyyar lashe dubbannin rayuka a Najeriya, bai kamata a ce ma yanzu ana fifita kabilanci ba. Don haka Shugaba Muhammadu Buhari, da yake mutum ne, wanda har yakin basasa ya yi,ya san tarihin kasar nan, kuma su masu kiraye-kiraye sun san matsawar Shugaba Muhammadu Buhari ne shugaban kasa to burinsu na ganin an dora Najeriya bisa doron kabilanci ba zai taba zama gaskiya ba.
Rukuni na biyu su ne wadanda ke so kawai Shugaba Muhammadu Buhari ya dauko gurbataccen rahotan taron kasa, wanda tsohon shugaban kasa GoodLuck Jonathan ya shirya a 2014 ya aiwatar cikin gaggawa. Taron da shi da kansa Jonathan ya ba da sunayen wakilan da za su kasance a wurin taron. Kazalika wakilan taron sun saba wa alkalumma al’ummar Najeriya, wanda kidayar shekarar 2006 ta nuna. MIsali, Kiristoci sun fi Musulmi yawa a wurin taron, sannan duk magoya-bayan jam’iyyar PDP ne da masu ra’ayin Gwamnatin Jonathan ne suka cika wurin taron. An kira su an tara su a kasaitattun otel-otel a Abuja, an ba su kudi domin daga karshe su amince da abin da Jonathan da mutanen Kudu ke so. Wannan ya sa rahotan taron ya yi daidai da muradun ‘yan-bokon kudu, kuma shi ya sa suke ta kiraye-kirayen dole sai Shugaba Muhammadu Buhari ya aiwatar da rahotan, abin da kuma in aka yi, to za a zalunci al’ummar Arewacin kasa ne kawai. Misaali, taron ya amince da a rage karfin gwamnatin tarayya, inda za a dauko wasu manyan ayyuka da gwamnatin tarayya ce kawai ke da hurumin yinsu a jibga ma jihohi.
Sannan ya amince da kirkiro sababbin jihohi da batun sauya yadda ake raba arzikin kasa. Duk wadannan wasu tsofaffin manufofi ne da ‘yan bokon Kudancin kasar nan ke son a aiwatar koda karfin tsiya ne. To mu mutanen Arewa, muna ganin a tafiyar da ake,yadda da kyar da jibin goshi wasu jihohin ke iya biyan albashi. Akwai jihohin da sai sun ciwo bashi daga bankuna sannan suke iya ayyuka,to sai ka je ka kwaso wasu sababbin ayyukan gwamnatin tarayya ka lafta musu. Kuma ka sauya yadda ake raba arzikin kasa, inda Kudancin kasar za su mallake rijiyoyin man fetur da manyan tasoshin jiragen ruwa, mu kuma Arewa a bar mu da noma da kiwo irin na zamanin jahiliyya. To muna ganin hakan zai kara gibi tsakanin jihohin Najeriya, inda jihohi masu arziki za su yi fintikau, can kuwa a gefe guda, matalautan jihohi za su kara nutsewa cikin tekun talauci.
So ake kuma gwamnatin tarayya ta koma ‘yar Rabbana ka wadata mu, inda sai ta yi bara wajen jihohi masu arziki kana za ta iya sauke nauyin da ke kanta. Kada mu manta wasu shekaru can baya, kasar Amurka ta taba aiwatar da irin wannan tsari, amma dole ta canza shi, saboda sai da ta kai ga gwamnatin tarayya ta ta yi bara wajen manyan jihohi, kafin ta iya biyan albashi da sauke nauyinta.
Muna tare da Buhari kan maganar Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa, wannan ba jayayya, duk mai son a sauya fasalin Najeriya, to ya tafi wajen danmajalisarsu.
Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina shi ne Babban Sakataren kungiyar Muryar talaka ta kasa 08165270879 [email protected]